fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Ansu Fati

Barcelona ta bayyana cewa tauraron dan wasanta Ansu Fati zai dauki tsawon watanni hudu yana jinya bayan ya samu rauni a kafar sa ta hagu

Barcelona ta bayyana cewa tauraron dan wasanta Ansu Fati zai dauki tsawon watanni hudu yana jinya bayan ya samu rauni a kafar sa ta hagu

Uncategorized, Wasanni
Tauraron dan wasan Barcelona mai shekaru 18, Ansu Fati ya samu rauni a kafar shi ta hagu yayin da suke karawa da Real Betis jiya wanda suka yi nasarar lallasa kungiyar 5-2 a gasar La Liga. Kuma kungiyar Barcelona ta sanar a ranar litinin cewa an yiwa tauraron dan wasan nata tiyata a kafar tasa kuma sai ya dauki tsawon watanni hudu yana jinya, wanda hakan ka iya kawowa Barca cikas a gasar zakarun nahiyar turai da kuma La Liga. Ansu Fati yayi nasarar cin kwallaye biyar kuma ya taimama wurin cin kwallye biyu a wasanni goma daya bugawa Barcelona a wannan kakar, Amma yanzu raunin daya samu yasa ba zai buga wasan sada zumunta tsakanin Sifaniya da Netherland ba,kuma zai rasa wasannin da Sifaniya zata kara da kasar Switzeland da Jamus a gasar kofin kasashen nahiyar turai.
Barcelona 4-0 Villarreal: Yayin da Ansu Fati ya taimakawa Barcelona da kwallaye biyu cikin mintina 20

Barcelona 4-0 Villarreal: Yayin da Ansu Fati ya taimakawa Barcelona da kwallaye biyu cikin mintina 20

Wasanni
Tauraron dan wasan Barcelona mai shekaru 17, Ansu Fati wanda yanzu ya samu damar shiga tawagar farko kuma aka bashi lamba 22 yayi nasarar cin kwallaye biyu a wasan Barcelona na farko a gasar La Liga na wannan kakar, kuma dan wasan Sifaniyan shine yasa Barcelona tayi nasara akan Villarreal. Ansu Fati ya zamo dan wasan daya fara ciwa Barcelona kwallo a wannan kakar sannan kuma ya zamo dan wasa na shida a gasar La Liga wanda ya ciwa kungiyar shi kwallo ta farko a gasar yana dan kasa da shekara 18. Fati ya haskaka sosai a wasan saboda cikin mintina 20 ya zira kwallaye biyu kuma a minti na 34 yayi sanadiyar penaritin da Messi yaci. Pedri da Trincao da tsohon dan wasan Juventus Pjanic duk sun fara bugawa Barcelona wasa a yau, yayin da Pedri ya canji Coutinho a minti na 69 kafin Trincao y...
Barcelona tayi burus da tayin da aka yiwa Ansu Fati na yuro miliyan 150

Barcelona tayi burus da tayin da aka yiwa Ansu Fati na yuro miliyan 150

Wasanni
Sabon wakilin Ansu Fati Jeorge Mendez shine ya sanar da Barcelona wannan kwantirakin na yuro miliyan 125 tare da karin yuro miliyan 25 idan dan wasan yayi kokari sosai amma Barcelona tayi burus da wannan tayin kuma taki amincewa ta fara tattaunawa akan siyar da dan wasan mai shekaru 17. A farkon wannan shekarar wata kungiya ta taya Ansu Fati a farashin yuro miliyan 100 kuma shima wannan tayin ta hannun Jeorge Mendez ya fito duk da cewa a lokacin ba shine wakilin dan wasan ba, amma Barcelona taki amincewa da siyar da dan wasan Sifaniyan kuma har ta saka mai farashin yuro milyan 400 domin kar wata kungiya tayi yunkurinn siyan shi. Mendez bai bayyana sunan kungiyar data taya Ansu Fati a farashin yuro miliyan 150 amma an samu labari daga kasar Ingila cewa Manchester United tana da ra'a...
Ansu Fati ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya bugawa Sifaniya wasa cikin shekaru 84

Ansu Fati ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya bugawa Sifaniya wasa cikin shekaru 84

Wasanni
A yaune kasar Jamus ta bugawa wasa da Sifaniya a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Turai. Wasan ya kare da sakamakon kunnen doki 1-1.   Tauraron dan wasan Sifaniya, Ansu Fati ne ya dauki hankulan mutane a wasan bayan da ya zama dan wasa mafi karancin shekaru,17 da ya bugawa kasar Sifaniya wasa a cikin shekaru 84 da suka gabata. Angel Zubieta ne na karshe mafi karancin shekaru da ya bugawa Sifaniya wasa a shekarar 1936. Ansu Fati ya ci kwallo amma aka kasheta saboda wata Keta da Sergio Ramos yayi.