
Dan Asalin Najeriya, Anthony Joshua ya doke Kubrat Pulev a Damben da suka yi
Dan damben Burtaniya Anthony Joshua ya doke Kubrat Pulev, wanda hakan ya kara fitowa da batun karawarsa da Tyson Fury fili.
Joshua ya yi nasara ne a fafatawar da aka kai zagaye uku ana yi.
'Yan kallo 1,000 ne aka bai wa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la'akari da daukar matakan bada tazara saboda annobar Korona.
Kuma jim kadan bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu ne magoya bayansa suka riƙa fadar cewa 'saura Fury'.
Furta hakan ke da wahala kuwa sai Anthony Joshua ya basu amsar cewa 'duk wanda ke da tarin kofuna ya zo na shirya'.
'Idan ma Tyson Fury ne, to shi ke nan a shirye nake in kara da Tyson Fury'.
Ba da wata wata ba kuwa sai shima Tyson Fury ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa 'to kun ji amsar Anthony Joshua...