
Shugaban NEDC ya ce za a kawar da kungiyar Boko Haram nan ba da jimawa ba
Duk da yawan kashe-kashen sojoji da fararen hula da 'yan tawaye ke yi a yankin Arewa maso Gabas, Shugaban Kwamitin Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC), Manjo-Janar Paul Tarfa (retd), ya yi hasashen cewa za a murkushe kungiyar Boko Haram nan gaba kadan.
Tarfa, wanda ya yi magana a jiya a Garkida, ma haifarsa dake jihar Adamawa, yayin da yake duba gine-ginen da 'yan tawayen suka kone kwanan nan, ciki har da gidansa, ya bayyana cewa Nan gaba kadan za a kawo karshen tashin hankula a kasar bisa al'kawarin gwamnatin tarayya da ta sabunta.
Ya fadawa 'yan jaridu cewa harin da kungiyar ta kai a kwanannan ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya zasu shafe su nan ba da jimawa ba.
Sa annan Shugaban NEDC, ya raba kayan agaji na miliyoyin nairori ga wadanda harin ya ritsa da su, ya bukace s...