fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Arfa

Ranar Alhamis Za A Gabatar Da Hawan Arfa A Saudiyya

Ranar Alhamis Za A Gabatar Da Hawan Arfa A Saudiyya

Siyasa
Hukumomin Saudiya sun bayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuli a matsayin ranar hawa Arafa, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Zul Hajji a yau Litinin, abin da ke nuna cewar gobe watan Zul Kida zai cika 30.   Kotun Kolin Saudiya ta ce ranar Laraba mai zuwa za ta zama ranar 1 ga watan Zul Hijja saboda cikar watan Zul Kida, abin da ya sa za a hau Arafat ranar Alhamis 30 ga watan Yuli. A karkashin wannan tsari, ranar Juma’a 31 ga watan Yuli ta kasance ranar babbar Sallah ko kuma Eid-el Adha.   Kimanin mutane dubu 1 ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus wadda ta tilasta wa mahukuntan Saudiya daukar matakin rage yawan mahajjata daga sassan duniya.