fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Arik

Kamfanin jirgin sama na Arik zai cigaba da zirga-zirga bayan dokar hana fita da gwamnatin Legas ta sassauta

Kamfanin jirgin sama na Arik zai cigaba da zirga-zirga bayan dokar hana fita da gwamnatin Legas ta sassauta

Tsaro
Kamfanin Jirage Na Arik Air Zai cigaba da Zirga-zirga biyo bayan dokar hana fita da Gwamnatin Jihar Legas ta sassauta   Shugabannin kamfanin jirage na Arik Air sun sanar da ci gaba da zirga-zirgar a ciki da wajen jihar Legas daga ranar 24 ga watan Oktoba, bayan sassauta dokar hana fita da Gwamnatin Legas ta sanya. Mista Adebanji Ola, wanda shine Manajan Sadarwa na Kamfanin jiragen shine ya sanar da hakan a ranar juma'a ga manema labarai.   Idan zaku iya tunawa gwamnatin jihar Legas ta sanya dokar hana fita na tsawan sa'o'i a jihar sakamakon zanga-zangar adawa da rundunar SARS wanda a karshe ta juye zuwa tashin hankali.
Kamfanin Jirgen Arik Air ya soke zirga-zirga A ranar Laraba sakamakon dokar hana fita A Jihar Legas

Kamfanin Jirgen Arik Air ya soke zirga-zirga A ranar Laraba sakamakon dokar hana fita A Jihar Legas

Tsaro
Biyo bayan sanya dokar hana zirga-zirga da Gwamnatin Jihar legas ta sanya na tsawan awanni 24 bayan shafe tsawan mako guda ana gudanar da zanga-zangar adawa da cin zarafin da rundunar SARS keyi. kamfanin Arik Air ya sanar da cewa ya soke dukkan ayyukansa na zirga-zirga a ranar Laraba 21 ga watan Oktoban 2020, saboda dokar hana fita na tsawan sa’o’i 24 da gwamnatin jihar legas ta sanar a ranar Talata, 20 ga watan da muke ciki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Manajan kamfanin jiragen ya fitar a ranar Talata.