fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Arsen

Dan wasan Arsenal Matteo Guendouzi ya kamu da cutar Covid-19

Dan wasan Arsenal Matteo Guendouzi ya kamu da cutar Covid-19

Kiwon Lafiya
Tauraron dan wasan Arsenal na tsakiya wanda ta baiwa kungiyar Hertha Berlin aro Matteo Guendozi ya kamu da cutar korona bayan ya dawo daga bugawa kasar sa faransa wasa. Dan wasan mai shekaru 21 yayi gwajin cutar har sau biyu kuma gabadaya sakamakon gwajin ya nuna cewa ya kamu bayan ya bugawa matasan faransa masu kasa da shekaru 21 wasa kuma zai cigaba da killace kanshi har na tsawon kwanaki 10. Guendouzi yana cikin koshin lafiya kuma babu wata alamar cutar a tattare da shi yayin da Hertha Berlin ta kara da cewa dan wasan bai sadu da sauran abokan aikin shi na kungiyar ba tun dawowar shi.