
Bukayo Saka ya taimakawa Arsenal ta fara jiyo kanshin gasar zakarun nahiyar turai
Kungiyar Arsenal na daf da kawo karshe shekaru biyar datayi ba tare da buga gasar zakarun nahiyar turai ba, bayan Bukayo Saka yaci mata kwallo guda ta doke Aston Villa daci daya mai ba haushi.
Nasarar Arsenal tayi tasa yanzu ta cigaba da zama ta hudu a saman teburin gasar Firimiya inda ta kerewa Manchester United da maki hudu, kuma duk da haka tanada kwantan wasa guda.
Arsenal tasha kashi daci 2-0 a hannun Liverpool wasanta daya gabata, amma yau ta daure damara ta dawo kan bakarta inda ta cigaba da samun nasara a wannan kakar.