fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Arsenal

Arsenal ba zata siyar da Nketiah a wannan watan ba>>Mikel Arteta

Arsenal ba zata siyar da Nketiah a wannan watan ba>>Mikel Arteta

Wasanni
Kungiyar West Ham ta gasar Premier na harin siyan Eddie Nketiah daga Arsenal domin ya maye mata gurbin Sebastein Haller wanda ta siyarwa Ajax a farashin yuro miliyan 20.2, kasa da rabin farashin yuro miliyann 45 data biya wurin siyan dan wasan daga Frankfurt. Amma yanzu an samu labari daga Arsenal ta hannun kocin ta, Mikel Arteta na cewa kungiyar Premier League din bata da niyyar siyar da Eddie Nketiah a wannan watan. Kocin West Ham David Moyes ya bayyana cewa basu taba tunanin siyar da Haller ba kafin Ajax ta fara harin siyan dan wasan, saboda ya taimaka masu wurin cin wasu yan wasanni, amma yanajin cewa canja sheka da Haller yayi abune mai kyau a wurin dan wasan.
Arsenal ta tabbatar da siyan Omar Rekik daga Hertha Berlin a farashin yuro 900,000

Arsenal ta tabbatar da siyan Omar Rekik daga Hertha Berlin a farashin yuro 900,000

Wasanni
Arsenal na shirin tabbatar da siyan dan wasan baya na kungiyar Hertha Berlin, Omar Rekik a farashin yuro 900,000 cikin wannan makon, yayin dan wasan mai shekaru 19 zai zamo dan wasa na farko da mikel Arteta ya siya a kasuwar yan wasa ta watan janairu. Omar Rekik dan wasan baya ne amma sai dai ba zai samu damar shiga tawagar farko a kungiyar Arsenal ba, yayin da Gunners suke shirin bayar da shi aro wa kungiyar Hertha saboda hakan zai taimaka mai wurin kwarewa sosai a wasan tamola. Amma a halin yanzu Arsenal bata kammala yanke shawara akan bayar da aron dan wasan ba acewar manema labarai na Football.london. Tuni dai a Rahotannin da Hutudole ke samu Arsenal  ta tabbatar da sayen dan wasan.
Kungiyar Nice zata aro dan wasan baya na Arsenal, William Saliba har izuwa karshen wannan kakar

Kungiyar Nice zata aro dan wasan baya na Arsenal, William Saliba har izuwa karshen wannan kakar

Wasanni
Kungiyar Arsenal zata bayar da aron dan wasanta na baya William Saliba wa kungiyar Nice ta gasar Ligue har izuwa karshen wannan kakar, amma sai dai bata baiwa kungiyar faransan zabin siyan shi ba saboda dan wasan yana cikin tsarukanta nan gaba. Kungiyar Arsenal ta siya William Saliba ne a farashi kusan yuro miliyan 27 daga kungiyar Saint Etienne a kakar data gabata, amma dan wasan mai shekaru 19 ya cigaba da taka leda a tsohuwar kungiyar tashi a matsayin aro. Saliba yana tare da tawagar Arsenal amma har yanzu bai fara biga masu wasa ba yayin da kuma baya cikin tawagar kungiyar da zasu buga mata wasanni a gasar Europa League. Kungiyar Saint Etienne ta kusa kara siyan tauraron dan wasan nata a wannan kakar amma sai dai ta samu tangarda a cikin yarjejeniyar tada Arsenal a watan...
Lacazette yayi nasarar cin kwallaye biyu yayin da Arsenal ta lallasa West Brom daci 4-0

Lacazette yayi nasarar cin kwallaye biyu yayin da Arsenal ta lallasa West Brom daci 4-0

Uncategorized
Kungiyar Arsenal ta koma ta 11 a teburin gasar Premier League bayan ta lallasa West Brom daci hudu ta hannun Tierney, Bukayo Saka da kuma Lacazette wanda yaci kwallaye biyu. Sakamakon wasan yasa yanzu Arsenal tayi nasara karo na uku kenan a jere bayan ta lallasa Chelsea daci 3-1 sai kuma ta lallasa Brighton daci 1 sannan kuma wasan ta na yau data lallasa West Brom daci har hudu.
Bani da tabbacin cewa ko Ozil zai dawo cikin tawagar Arsenal>>Mikel Arteta

Bani da tabbacin cewa ko Ozil zai dawo cikin tawagar Arsenal>>Mikel Arteta

Wasanni
Tauraron dan kasar Jamus dake taka leda a kungiyar Arsenal, Mesut Ozil bai bugawa kungiyar tashi wasa ba tunda aka fara buga wannan kakar, yayin da shima abokin aikin shi Sokratis ya rasa damar bugawa kungiyar wasa a wannan kakar. Ozil har yanzu yanada sauran kwantirakin watanni 6 a kungiyar Arsenal yayin da kuma yake daukar albashi mao tsoka na yuro 350,000 a kowane mako. Kocin kungiyar Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewa zasu siyar da wasu yan wasan daba sa cikin tsarukan su a wannan kasuwar da aka bude jiya ta yan wasa, amma ba zasu sokema wani dan wasa kwantiraki ba. A karshe kocin ya kara da cewa har yanzu bashi da tabbacin cewa ko vOzil zai dawo cikin tawagar Arsenal a wannan watan, amma koma dai meye zasu ga yadda al'amuran zasu kasance a kasuwar yan wasa.
A karo na farko Arsenal tayi nasarar cin wasanni biyu a jere tun farko wannan kakar, bayan ta lallasa Brighton 1-0

A karo na farko Arsenal tayi nasarar cin wasanni biyu a jere tun farko wannan kakar, bayan ta lallasa Brighton 1-0

Wasanni
Kungiyar Arsenal tayi nasarar komawa ta 13 a teburin gasar Premier League bayan taci galaba akan Brighton ta hannun Andre Lacazette wanda yaci kwallo cikin dakiku 25 da shigowar wasan daga benci. Arsenal tayi nasarar doke Brighton ne bayan ta lallasa Chelsea daci 3-1 a wasanta daya gabata, wanda hakan yasa ta samu nasara sau na biyu a jere karo na farko tun bayan data yi hakan a farkon wannan kakar. Kiris ya rage kungiyar Brighton ta fara jagorancin wasan kafin aje hutun rabin lokaci, amma bayan bayan an dawo daga hutun Arsenal tayi nasarar zira kwallo guda ta hannun Lacazette wadda tasa yanzu Brighton take daf da fadawa Relagation. https://twitter.com/Arsenal/status/1344048232792518658?s=19
Kungiyar Arsenal tana harin siyan Diego Costa daga Atletico Madrid

Kungiyar Arsenal tana harin siyan Diego Costa daga Atletico Madrid

Uncategorized
Rahotanni daga kasar sifaniya sun bayyana cewa tauraron dan wasan Atletico Madrid, Diego Costa ya bukaci kungiyar ta soke mai sauran watanni shida na kwantirakin shi akan lokaci yayin da kwantirakin zai kare nan da watan yuni a shekara ta 2021. Kungiyar Arsenal tana daya daga cikin kungiyoyin dake harin siyan dan wasan yayin da aka samu labari daga As Diario cewa Atletico bata da niyyar siyar da shi wa abokan hamayyar ta, kuma hakan zai iya ba Arsenal damar siyan shi saboda da basa cikin gasar zakarun nahiyar turai. Tsohon dan wasan Chelsen mai shekaru 32 yana so ya cigaba da murza leda ne a nahiyar turai, yayin da yake shan gwagwarmaya a wannan kakar bayan ya samu raunika sannan kuma yanzu Suarez da Felix sun zamo mayan yan wasa gaba na tawagar Simone.
Gabriel ya kamu da cutar sarkewar numfashi (Coronavirus)>>Arsenal

Gabriel ya kamu da cutar sarkewar numfashi (Coronavirus)>>Arsenal

Wasanni
Tauraron dan wasan baya na kungiyar Arsenal, Gabriel Magalhaes bai buga wasa tsakanin Arsenal da Chelsea ba sakamakon an umurce shi daya killace kanshi bayan ya kusance mutumin daya ke dauke da cutar sarkewar numfashin. Kungiyar Arsenal ta tabbatar da cewa dan wasan nata ya kamu da cutar yayin da kuma hakan zai sa shi ya rasa wasannin ta guda biyu masu zuwa na ranar talata da kuma sati, wanda zasu kara da Brighton da kuma West Brom. A karshe kungiyar ta kara da cewa dan wasan nata zai cigaba da killace kanshi tare da bin sharuddan gwamnatin kasar Ingila dama gasar Premier League bakidaya.
Bidiyon Arsenal 3-1 Chelsea: Yayin da Granit Xhaka ya zamo dan wasa na farko daya ciwa Arsenal kwallon nesa (Free kick)tsakanin ta Chelsea tun shekara 2004

Bidiyon Arsenal 3-1 Chelsea: Yayin da Granit Xhaka ya zamo dan wasa na farko daya ciwa Arsenal kwallon nesa (Free kick)tsakanin ta Chelsea tun shekara 2004

Wasanni
Kungiyar Arsenal ta kunyata Chelsea bayan ta karbi bakuncin ta kuma tayi nasarar lallasa ta daci 3-1,ta hannun Granit Xhaka da Bukayo Saka da kuma Lacazette wanda ya kasance dan wasan daya fi zira mata kwallaye masu yawa a wannan kakar. Kwallon nesan (Free kick)da Granit Xhaka yaci tasa yanzu ya zamo dan wasa na farko daya ciwa Arsenal kwallon nesa tsakanin tada Chelsea tun bayan Thierry Henry a shekara ta 2004, yayin shi kuma Lacazette ya zamo dan wasa na farko daya ciwa Arsenal bugun daga kai sai gola tsakanin su da Chelsea tun bayan Gilberto Silva a shekara ta 2007. Tauraron dan wasan Chelsea, Tammy Abraham ne yayi nasarar ciwa Lampard kwallo guda a wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, yayin da shi kuma Timo Werner ya buga wasanni 10 ba tare da ciwa kungiyar shi kwal...
Kocin West Ham ya bayyana cewa Arsenal abokiyar takarar shi ce wurin gujewa fadawa Relegation a gasar Premier League

Kocin West Ham ya bayyana cewa Arsenal abokiyar takarar shi ce wurin gujewa fadawa Relegation a gasar Premier League

Wasanni
Sabon kocin West Ham, Allerdyce zai jagoranci tawagar tasa su ziyarci kungiyar zakarun kasar Ingila ranar sati wato Liverpool, yayin da maki bakwai kacal West Ham ta samu a wasanni 14 data buga na gasar Premier League. Wanda hakan yasa kungiyar ta kasance ta biyu a kasan teburin gasar Premier League kuma take fafatawa domin samun matsugunni a gasar. A ranar laraba Allerdyce ya bayyanawa manema labarai cewa ya kamata kungiyar shi ta gujewa shan kashi a hannun kungiyoyi 8 dake kasan teburin gasar idan har suna so su samu nasara a wannan kakar. Yayin da kuma ya kara da cewa hatta Arsenal wadda ta kasance ta 15 a teburin gasar da maki 14 abokiyar takarar shi ce wurin samun matsugunni a babbar gasar ta kasar Ingila domin gukewa fadawa Relegation. Kocin ya kara da cewa lallasawar da Man...