
Arsenal zata iya lashe kofin Premier League a karkashin jagorancin Mikel Arteta>>Arsene Wenger
Arsenal tana da maki tara tun da aka fara buga wannan kakar yayin data kasance ta hudu a saman teburin gasar Premier League kuma maki uku ne tsakanin ta da Everton wanda suka kasance a saman teburin gasar. Arsenal zata buga wasan ta na gaba da Manchester City ranar sati kuma Arsene Wenger ya bayyana cewa Arteta yanada tawagar mai karfi wadda zata iya kawo karshen shekaru 16 da kungiyar tayi tana kwadayin lashe kofin Premier League.
Tsohon kocin Arsenal din ya bayyana cewa tabbas Arsenal zata iya lashe kofin Premier League a karkashin jagorancin Mikel Arteta saboda sun kashe kudade a shekaru biyu da suka gabata kuma Arteta yanada tawaga mai karfi tare da gwarazan yan wasa masu bin umurnin kocin nasu.
Arsene Wenger ya bar kungiyar Arsenal a karshen kakar 2017/2018 kuma dan kasar far...