fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Asiwaju Bola Ahmad Tinubu

“Ba zai yiyu ka kira matasa malalata ba alhalin ba’a basu ingantacciyar wutar lanyarki ba”>>Tinubu ya caccaki gwamnatin Buhari

“Ba zai yiyu ka kira matasa malalata ba alhalin ba’a basu ingantacciyar wutar lanyarki ba”>>Tinubu ya caccaki gwamnatin Buhari

Breaking News, Siyasa
Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari a jiya ranar sati yayin dayake yakin neman zabe a kudancin kasar nan. Yayin daya bayyana cewa ba zai yiyu gwamnati ta kira matasa malalata ba alhalin bata bayar da ingantacciyar wutar lantarki ba. Inda ya kara da cewa Najeriya nada albarka sosai da har zata iya samarwa kanta wutar lantarki kuma ta baiwa wasu kasashe a nahiyar turai. Shekaru hudu baya ne shugaba Buhari ya kira matasan Najeriya malalata a wani taron da suka gudanar na shuwagabanni a Ingila, yayin da Tinubu ya bashe amsar maganar tashi a jiya inda yake yakin neman zabe.
Muhammadu Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 70

Muhammadu Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 70

Siyasa
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari tare da sauran shuwagabanni da kuma membobin APC sun taya tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu murnar cika shekara 70. Mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawarwari ta fannin kafafen sada zumunta, Femi Adisina ne ya bayyana hakan ranar litinin. Inda yace shugana Buhari ya yabi Tinubu sosai bisa namijin kokarin dayake yi a jam'iyyar APC, kuma yayi mai addu'a Allah ya kara mai lafiya da misan kwana.
Yunwa ta ishi ‘yan Nageria, a daina kame-kame a basu tallafi kawai>>Tinubu ya gayawa Buhari

Yunwa ta ishi ‘yan Nageria, a daina kame-kame a basu tallafi kawai>>Tinubu ya gayawa Buhari

Siyasa, Uncategorized
Babban jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yunwa ta ishi 'yan Najeriya kuma sun gaji, an haka a daina kame-kame kawai a basu tallafi.   Ya bayyana hakane a wajan taron bikin cikarsa shekaru 69 da aka yi a Kano.   Tinubu yace saboda matsin da aka shiga, kasar Amurka ta warewa jama'arta Tallafin Dala Tiriliyan 1.9, kuma tana shirin kara basu wani tallafin. Yace irin abinda ya kamata Najeriya ta kwaikwaya kenan. “It is time to put stimulus in place. This is no time for austerity. I hope you listen carefully. This is not the time to constrain the economy. This is the time to create the opportunity. “If you hear America spending $1.9tn and they are not looking back and they are still asking for $3tn for infrastructure ...
Na zabi Kano dan yin bikin zagayowar ranar Haihuwata saboda in nuna cewa Fulani da Yarbawa kansu hade yake>>Tinubu

Na zabi Kano dan yin bikin zagayowar ranar Haihuwata saboda in nuna cewa Fulani da Yarbawa kansu hade yake>>Tinubu

Siyasa
Tsohon Gwamman Legas Kuma Jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya zabi yayi murnar zagayowar Ranar haihuwarsa a Kano ns dan ya nuna cewa Yarbawa sa Hausawa kansu a hade yake.   Ya bada Misalin yanda diyar gwamnan Kano, Fatima Ganduje ta auri dan Gwamnan Oyo inda yace hakan alamace me nuna akwai kyakkyawar Alaka tsakanin Yarbawa da Hausawa. “It is to demonstrate to Nigerians at this critical time. It is because there is a Fulani man, a herder man who gave his daughter to a farmer, Yoruba man. And that Fulani, that Yoruba (sic), and some people are agitating wrongly.”
Wasu dai fatansu su ga shugaba Buhari da Tinubu sun bata, kuma hakan ba zai faru ba>>Gwamna Badaru

Wasu dai fatansu su ga shugaba Buhari da Tinubu sun bata, kuma hakan ba zai faru ba>>Gwamna Badaru

Siyasa
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta rashin jituwa tsakanin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu. A hirarsa da Channelstv, Badaru ya bayyana cewa, an kawo labarin ne kawai dan saka rudani tsakanin mutane.   A Baya dai, hutudole.com ya kawo muku Rahoton cewa, Gwamna Badaru yace ba ba'a taba shugaba kamar Buhari ba Badaru yace mutane na son ganin an samu Baraka tsakanin Shugaba Buhari da Tinubu amma burinsu ba zai cika ba. Yace APC tsintsiyace madaurinki daya.   “I think people wanted to see that and that will not happen. I believe it is all politics. President Muhammadu Buhari, Bola Tinubu and all the leaders of the party speak with one voice.   “We have pushed that story about President Bu...
An kwantar da Tinubu a Asibiti

An kwantar da Tinubu a Asibiti

Siyasa
An samu Rahoton cewa tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu na can kasar Faransa kwance a Gadon Asibiti babu lafiya.   The Cable ta ruwaito cewa amma ba kamar yanda ake yadawa ba, Tinubu bai kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 ba. Majiyar ta bayyana cewa Tinubu ya je kasar wajenne dan hutawa kamar yanda ya saba yi duk shekara.
Majalisar Malamai ta jihar Kano ta musanta zargin da ake mata na goyan bayan takarar Bola Tinubu a kakar zabe mai zuwa

Majalisar Malamai ta jihar Kano ta musanta zargin da ake mata na goyan bayan takarar Bola Tinubu a kakar zabe mai zuwa

Siyasa
Shugaban Majalisar malamai Malam Ibrahim Khalil shine ya musanta wannan zargi a yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano. Malamin ya ce, ko kadan babu wannan maganar hasalima ya cika da mamakin masu yada wannan batu. A cewarsa, Majalisar Malamai bata goyan bayan wani Dan takara, inda ya kara da cewa Bola Tinubu ya zo ne jahar kano domin halartar taron bikin aure. Idan zaku tuna Jigo a jam'iyyar APC Ahmad Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Kano a makon da ya gabata domin halartar taron bikin aure da aka gudanar a jihar na 'ya ga shahrararan malamin Addinin Musulunci Bin Usman lamarin da ya janyo cece kuce.    
Ina tsaka mai wuya duk sai dora min laifi ake ta ko ina>>Tinubu

Ina tsaka mai wuya duk sai dora min laifi ake ta ko ina>>Tinubu

Siyasa
Bola Ahmad Tinubu,  Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC ya bayyana cewa bashi da hannu a harbe-harben da suka faru a Lekki Toll Gate dake jihar.   Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar inda yace bashi da hannun jari a Lekki sannan kuma ba shine ya sa aka kai sojojin da suka yi harbe-harbe ba. Tinubu yace shi ya shiga tsaka mai wuya akan lamarin rikicin inda wasu sun zargeshi da cewa shine ya dauki nauyin zanga-zangar SARS sannan daga baya kuma aka zargeshi da hannu a harbe-harben Lekki.   Yace tabbas yana da hannun jari a TheNation da kuma gidan talabijin na TVC kuma ya san cewa za'a kai musu hari amma saboda baya son zubar da jini shiyasa bai ce a kai jami'an tsaro wajan ba.   Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta kulle Lekki To...