
Masu neman Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 sun kai miliyan 1
Wasu masu goyon bayan tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyya me mulki, Bola Ahmad Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 na ci gaba da fafutuka.
To saidai har zuwa yanzu, Tinubu be bayyana ra'ayin tsayawa takarar ba. Ya bayyana cewa yayi wuri kuma yanzu abinda ya mayar da hankali akai shine baiwa gwamnatin shugaba Buhari shawara.
Shugaban kungiyar da ake kira TNN, Kunle Akunola ya bayyana cewa kungiyar yanzu tana da membobi a kasashe 13 kuma duk wani bata suna ba zai hana Tinubu darewa kan mulkin Kasarnan ba.