fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Asiya Ahmad

Asiya Ahmad: Jarumar da tun tana yarinya Adam Zango ke sonta, kiris ya rage su yi aure amma Allah bai yi ba

Asiya Ahmad: Jarumar da tun tana yarinya Adam Zango ke sonta, kiris ya rage su yi aure amma Allah bai yi ba

Nishaɗi
ASIYA Ahmad ta na daga cikin matasan jarumai mata da su ka yi fice a Kannywood. Jarumar, wadda ake yi wa laƙabi da Asiya Maikyau, ƙanwa ce ga fitacciyar 'yar wasan nan Samira Ahmad. Ya zuwa yanzu, Asiya ta samu kamar shekara biyar da fara yin aktin. Kuma ta shigo ne da ƙafar dama, saboda a lokacin da ta fara an yi wasoson ta. Hakan bai rasa nasaba da cewa da gaske mai kyau ce, santala, doguwa, wato dai son kowa ƙin wanda ya rasa. Haka kuma ga shi ta yi sabo da yawancin 'yan fim saboda yayar ta Samira da mijin yayar a lokacin da ta shigo, wato fitaccen jarumi kuma mawaƙi, T.Y. Shaban. 'Yan fim da dama na zuwa gidan su. Bugu da ƙari, Asiya ta yi iya aktin ƙwarai da gaske, sannan ta shigo a daidai lokacin da furodusoshi da daraktoci su ke buƙatar matasan jarumai mata iri...