
Yanda aka gano akwai Aljanu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock
Tsohon kakakin shugaban kasa a zamanin mulkin Goodluck Jonathan da kuma Olusegun Obasanjo, Doyin Okupe ya tabbatar da cewa akwai Aljanu a fadar shugaba kasar ta Aso Rock.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Vanguard inda yace amma fa aljanun ba daga cikin fadar suke ba.
A baya ma dai Tsohon hadimin shugaban kasa, Reuben Abati ma ya tabbatar da cewa, Akwai Aljanu a fadar shugaban kasar ta Aso Rock.
Hakanan hutudole.com ya ruwaito muku yanda PDP tace zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ya nuna shugaba Buhari zai iya zama a Najeriya ba tare da yawace-yawace ba
Okupe yayi dariya da aka masa tambayar amma yace, maganar gaskiya daga kauyuka da jihohi Aljanun suke fitowa.
Laughs…. No. I have read that people say that when y...