
Aston Villa ta kammala yarjejeniya akan siyan Emiliano Buendia daga Norwich City
Aston Villa ta kammala yarjeje da Norwich City akan siyan dan wasanta na tsakiya Emiliano Buendia.
Arsenal na harin siyan dan wasan amma Villa ta doke ta tayi nasarar shawo kan dan wasan Argentinan ya amince da ita. Kuma har Villa ta tabbatar da cewa tayi nasara wurin siyan dan wasan wanda ya lashe kyautar gwarzon gasar Championship a wannan kakar.
Farashin dan wasan ya kai yuro miliyan 33 wanda hakan yasa ya kasance dan wasa mafi tsada da Aston Villa ta siya a tarihi, kuma farashin ka iya kaiwa yuro miliyan 40 idan kwalliya ta biya kudin sabulu.
Yayin da ita kuma Norwich City zata kwashe riba sosai akan dan wasan domin yuro miliyan daya kacal ta siyo shi a shekarar 2018 daga Getafe.
Aston Villa agree deal to sign Norwich star Emiliano Buendia
Aston Villa have reached an a...