
“Zamu cigaba da zama a gida da yunwa har shekarar 2023”>>ASUU ta fadawa gwamnati
Kungiyar malaman kwalejn kimiyya da fasa ta jami'a watau ASUU, a jihar Calabar ta bayyana cewa ashirye suke su cigaba da zama a gida da yunwa idan gwamnati bata biya masu bukatun su ba.
Shugaban jami'ar Calabar ta UNICAL, Dr Edor J. Edor ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai na Daily Trust.
Inda yayi tsokaci akan maganar da Buhari yayi na cewa su dubi halin da dalibai suke ciki su janye yajin aiki, amma yace ba zasu janye ba kuma ashirye suke su kai shekrar 2023 suna yajin aikin.