
“Na gana da shugaba Buhari akan maye gurbinsa”>>Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ha bayyana cewa ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan maye gurbinsa a shekarar 2023.
Tsohon gwamnan jihar Legas din ya bayyan hakan ne a taron daya gudanar tare da membobin APC a majalisar wakilai.
Inda ya kara da cewa shi kadai ne tsayayyen mutumin dake neman takarar shugabanck a kasar sauran duk wasa ne. Kuma ya gana da Buhari cikin raha da jin dadi.