fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Atiku Bagudu

Shugaba Buhari ya cika Alkawarin da ya dauka na samar da Tsaro>>Gwamnan Kebbi

Shugaba Buhari ya cika Alkawarin da ya dauka na samar da Tsaro>>Gwamnan Kebbi

Siyasa
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari  ya cika alkawura 3 da yawa 'yan Najeriya a lokacin yakin neman zabensa.   Bagudu ya bayyana hakane a sakon Sallar da ya fitar ga mutanen jihar inda yace su kansu shaida ne kan tsaron da ake samu a Najeriya inda yace jihar tasa na daya daga cikin jihohi mafiya zama Lafiya a kasarnan. Ya bayyana cewa a yanzu babu wani guri dake hannun Boko Haram kamar yanda shugaba Buhari ya tarar. Ya kuma kara da cewa, shugaban ya samu nasara wajan farfado da tattalin arzikin Najeriya.   Sannan wajan yaki da cin hanci, shugaban ya ciri tuta. Bagudu ya godewa shugaba Buhari kan yadda da Abubakar Malami a matsayin na hannun damarsa wanda daga jihar ya fito.