fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Atletico Madrid

Atletico ta baiwa Chelsea damar aron dan wasanta Saul Niguez

Atletico ta baiwa Chelsea damar aron dan wasanta Saul Niguez

Wasanni
Saul na daya daga cikin yan wasan da suka lashewa kungiyar Atletico Madrid kofin La Liga a kakar bara, amma yanzu zata bar shi ya sauya sheka. Dan wasan mai shekaru 26 ya bugawa Atletico wasanni sama da 300 tun bayan daya samu damar shiga tawagar farko ta kungiyar yana dan shekara 17 a shekarar 2012. Yayin da itama Manchester United keda ra'ayin siyan dan wasan tare da Eduardo Camavinga na kungiyar Rennes. Saul Niguez: Chelsea among clubs offered Atletico Madrid midfielder on loan Saul was part of Diego Simeone's title-winning side last season but will be allowed to leave the club this summer. The 26-year-old has made more than 300 appearances for Atletico since breaking into the first team as a 17-year-old in 2012. Manchester United have been watching the midfielder, along w...
Bidiyon yanda Dembele ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da Atisaye

Bidiyon yanda Dembele ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da Atisaye

Wasanni
Tauraron dan kwallon Atletico Madrid,  Moussa Dembele ya yanke jiki ya fadi kasa yayin da suke Atisaye shi da abokan aikinsa.   Dembele na Aro ne daga Lyon wanda kuma zuwa yanzu wasanni 4 ya bugawa Atletico Madrid. Wannan yasa wasu ke ganin cewa bai taka rawar gani ba. Atletico Madrid na da damar sayensa idan suna so.   Lamarin ya farune ranar Talata da yamma sanda suke Atisaye.   Daga baya dai likitoci sun dubashi kuma ya dawo hayyacinsa wanda ma da kanshi ya tuka motarsa zuwa gida.   https://www.youtube.com/watch?v=EOQ5IaepIB0    
Valencia 0-1 Atletico Madrid: yayin dan wasan Valencia Lato yayi kuskuren ciwa Atletico kwallo guda

Valencia 0-1 Atletico Madrid: yayin dan wasan Valencia Lato yayi kuskuren ciwa Atletico kwallo guda

Uncategorized, Wasanni
Kungiyar Atletico Madrid ta cigaba da samun nasarar a wannan kakar yayin da yau ma ta lallasa Valencia 1-0 a gasar La Liga wanda hakan yasa makin ta ya kasance daidai dana Real Sociedad 23 wadda ta kasance a saman teburin gasar. Dan wasan Valencia Lato ne yayi kuskuren ciwa Atletico kwallon wadda tasa Diego Simone yayi nasarar lashe ganadaya maki uku na wasan. Itama kungiyar Elche da Cadiz sun raba maki bayan da suka tashi 1-1 duk dai a gasar ta La Liga.
A karin Farko, Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona:Bidiyon Kuskuren da Golan Barca ya tafka da ya jawo aka ci su kwallon

A karin Farko, Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona:Bidiyon Kuskuren da Golan Barca ya tafka da ya jawo aka ci su kwallon

Wasanni
Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona a wasan da suka buga jiya da ci 1 me ban haushi. Yannick Carrasco ne ya ciwa Atletico Madrid kwallonta bayan dawowa daga hutu Rabin Lokaci.   Wannan nasara ta Atletico Madrid akan Barcelona itace irin ta ta farko cikin kusan sama da shekaru 10 da suka gabata.   Nasarar ta baiwa Atletico Madrid damar komawa ta 2 a saman teburin gasar La Liga da maki 20, daidai dana Real Sociedad dake saman Teburin.   Golan Barcelona, Marc Andre ter stergen ne ta tafka gagarumin kuskuren da yasa aka ci kungiyar kwallo, inda ya fito cikin fili ya bar ragarsa.   Sau 5 kenan golan yana kuskuren da ke kaiwa ana cin kungiyar tasa tun daga watan Afrilun 2019 da ya gabata zuwa yanzu. A gasar La Liga,  babu golan da ya kaishi aik...
Atletico Madrid ta samu nasara a wasannin La Liga guda 23 a jere karo na farko a tarihi bayan ta lallasa Cadiz 4-0

Atletico Madrid ta samu nasara a wasannin La Liga guda 23 a jere karo na farko a tarihi bayan ta lallasa Cadiz 4-0

Wasanni
Tauraron dan wasan Atletico Madrid Jao Felix yayi nasarar cin kwallaye guda biyu yayin da Marcos Llorente da Luiz Suarez suka kara ciwa Diego Simone kwallaye biyu a wasan da suka lallasa Cadiz 4-0 jiya a gasar La Liga. Nasarar da Atletico Madrid suka yi tasa yanzu sun buga wasannin La Liga guda 23 a jere ba tare da cisu a wasan ba karo na farko a tarihin su, kuma yanzu sun komn saman teburin gasar da maki 17. Atletico Madrid tayi nasarar cin wasannin ta guda hudu a cikin wasanni biyar da suk gabata tun bayan da kungiyar Bayern Munich ta lallasata 4-0 a gasar zakarun nahiyar turai.
Yanzu-Yanzu:Suarez ya amince da komawa Atletico Madrid

Yanzu-Yanzu:Suarez ya amince da komawa Atletico Madrid

Wasanni
Rahotanni daga kasar Sifaniya na cewa tauraron dan kwallon kungiyar Barcelona, Luiz Suarez ya amince da komawa Atletico Madrid.   Rahoton yace Suarez da Atletico Madrid sun tattauna kuma shi akan kansa ya amince zai koma kungiyar. Nan da 'yan Awanni ake sa ran za'a kammala cinikin wanda Suarez zai koma kungiyar a kyauta.   Hakanan akwai Rahotannin dake cewa Juventus na tattaunawa da Atletico Madrid dan daukar dan wasanta, Alvaro Morata akan Aro da damar sayensa nan gaba.
Yan wasan Atletico Madrid guda biyu sun kamu da cutar Covid-19

Yan wasan Atletico Madrid guda biyu sun kamu da cutar Covid-19

Wasanni
Tawagar kungiyar Atletico Madrid da zasu yi tafiya izuwa garin Libson dake kasar Portugal sun yi gwajin cutar korona kafin su gudanar da atisayi ranar sati, kuma sakamakon gwajin ya fito ranar lahadi yayin daya bayyana cewa mutane biyu sun kamu da cutar kuma gabadayan su yan wasa ne. Yan wasan guda biyu sun killace kansu bayan an tabbatar da cewa sun kamu da cutar, kuma yanzu kungiyar tana shakkar cewa watakila wani kamu cikin sauran mutane 93 da zasu yi tafiya izuwa garin Libson ranar litinin domin su cigaba da buga sauran wasannin gasar zakarun nahiyar. Za'a sake yiwa gabadaya tawagar gwajin cutar ranar litinin wanda hakan zai sa su jinkirta tafiyar tasu saboda sai sun jira sakamakon sabon gwajin da suka yi kafin su yanke shawara.
A karin farko cikin shekaru 14, An Fitar da Liverpool daga gasar Champions League a matakin kungiyoyi 16

A karin farko cikin shekaru 14, An Fitar da Liverpool daga gasar Champions League a matakin kungiyoyi 16

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sha kashin ban mamaki a hannun Atletico Madrid data bita har gida,Anfield ta mata ci 3-2 a daren Laraba.   Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Wijnaldum wadda ta so ta makale, ta kara kwallo ta 2 ta hannun Firmino.   Saidai Atletico Madrid ta farke duka kwallaye 2 ta hannun Llorente inda ta kara kwallo ta 3 ta hannun Morata.   Wannan na nufin Liverpool ta sha kashi da jimullar kwallaye 4 kenan a hannun Atletico Madrid,  Gida dawaje.   Wannan ne karon farko da aka fitar da Liverpool daga gasar Champions League a matakin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar cikin shekaru 14 da suka gabata.   Tun bayan da Wani yaro dan shekaru 10 magoyi  bayan Manchester United ya yiwa Liverpool baki kan cewa ba za...