
Bafarawa ya kaiwa Kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila sunayen mutane da Rikici ya rutsa dasu a Arewa inda yace a biyasu diyya kamar yanda akawa masu zanga-zangar SARS
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya cika maganar da yayi a baya ta nemawa wanda rikice-rikicen Arewa ya shafa Diyya.
Ya kaiwa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ziyara inda ya mika masa sunayen mutanen da rikice-rikicen Arewa suka shafa sannan ya nemi a biya diyyarsu.
Bafarawa yace ya samo sunayenne daga kungiyoyi masu zaman kansu da suke da ikon kaiwa inda rikice-rikicen ke faruwa a Arewa. Yace yana jinjinawa kakakin majalisar saboda kokarin da yayi wajan ganin an biya wanda zanga-zangar SARS ta rutsa dasu diyya da kuma musu Adalci.
A nasa bangaren, Femi Gbajabiamila ya godewa Bafarawa da ziyara sannan kuma ya bashi tabbacin cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajan ganin an tabbatar da wannan bukata.
...