
Labaran kasuwar kwallon kafa: Manchester United da Chelsea da Arsenal sun ziyarci kasuwar yan wasan domin su kara da Man City da kuma Liverpool a kakar wasa mai zuwa
Zakarun gasar premier league wato Liverpool suna harin siyan dan wasan baya na kungiyar Schalke Ozan Kabak, wanda kungiyar shi ta sa mai farashin euros miliyan 40. Da yiwuwar Schalke zasu siyar da shi kasa da wannan farashin saboda rashin kudi amma sai dai Liverpool suna da abokan hammaya wajen siyan shi kamar Man City, Juventus da Dortmund.
United suna tattaunawa da Dortmund akan Jadon Sancho, amma sai dai United sun rage kusan euros miliyan 10 zuwa 15 cikin farashin dan wasan na kusan euros miliyan 90. Saboda rashin kudin siyan Sancho, United suna harin siyan dan wasan Villa Grealish. An gayama Jack cewa ba dole ne ya samu buga wasa a kowane mako ba,amna wannan ba zai hana kaftin din Villa kokawa kungiyar da zata habaka mai sana'ar shi da kudaden shi ba.
Arsenal...