fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: aure

Gwamnatin jihar Kano Ta Ware Naira Miliyan 245 Don Aurar da Mutanen Jihar Mabukata

Gwamnatin jihar Kano Ta Ware Naira Miliyan 245 Don Aurar da Mutanen Jihar Mabukata

Auratayya
Gwamnatin Jihar Kano a Nigeria ta zartas da ware kudade da suka kai Naira Miliyan 245 don tallafawa dimbin  mata da  maza da suka kai minzalin yin aure amman babu wuri, don su yi aure da tallafin aljihun Gwamnati. Kwamishinan Watsa labarai na jihar Malam Mohammed Garba ya sanar da haka  a cikin wata sanarwa a Kano Asabar. Kazalika ya fadi cewa an ware wasu kudaden Naira Miliyan 244 don baiwa kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars. Sanarwar na cewa Gwamnatin ta kuma ware kudade Naira Miliyan 29.3 don yiwa dabbobi alluran rigakafin cutuka wanda aka dakatar da yi shekaru uku da suka gabata. Har ila yau yace an ware wasu kudaden da suka kai Naira biliyan 1.2 don gyara hanyar Ahmadu Bello Way, dake Kano sai kuma wasu Naira miliyan 212.9 don gyara rukunin dakunan mata na...
Mata ta kai Mijinta kara saboda yawan jima’i,  Kotu ta raba auren

Mata ta kai Mijinta kara saboda yawan jima’i, Kotu ta raba auren

Auratayya
Kotun dake Mapo, Ibadan ta kashe auren wata mata, Basirat Adeyoyin da Mijinta, Adeyoyin Niyi saboda yawan jima'i da kuka zargin tsafi.   Mai shari'a na kotun, Ademila Odunade ya kashe auren wanda yace akwai yiyuwar lamura su baci idan ba'a yi hakan ba.   Ya kuma baiwa matar rikon yara 2 da ma'auratan suka haifa inda yace mijin ya rika bata Dubu 10 duk wata wanda zata rika kula da yaran dasu.   A jawabinta ga Alkali, Basirat tace suna zaune kwatsam sai ga mijinta yazo mata cewa wai ya samu wani bayanin da aka mai na cewa sai ya jera kwanaki 7 yana jima'i da ita ba kakkautawa.   Tace ta kasa fahimtar abinda yake nufi amma ta yadda. Tace a lokacin tana dauke da cikin wata 3, a rana ta 2 da suka fara wannan jima'i sai cikin nata ya zube. Tace taje As...
Hotuna:Kalli yanda dan shekaru 15 ya auri ‘yar shekaru 22

Hotuna:Kalli yanda dan shekaru 15 ya auri ‘yar shekaru 22

Auratayya
Wannan wani yarone me suna Abraham Samuel da ya auri masoyiyarsa me shekaru 22 a jihar Abia.   An daura auren masoyanne a karshen makon daya gabata, Ranar Lahadi, 27 ga watan Afrilun shekarar 2020.   Samuel shine kadai da a wajan mahaifinsa da ya rasu a shekarar 2010. Mazauna Garin da lamarin ya faru, Amaiyi Igbere dake karamar hukumar Bende a jihar sun bayyana mamakinsu da wannan lamari,musamman ganin yaron yayi karami da yawa.   Mahaifiyarshi ma dai tace kawai tirsasamata dangin mahaifinsa suka yi ta amince da auren.  
‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

Auratayya
Wani manomi dan shekaru 35 da haihuwa kuma mai wakiltar mazabar Iwogu a karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa, Ibrahim Kasimu Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah, ya auri wasu mata biyu a rana daya. Ya auri Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Isyaku Akose a ranar 28 ga Maris, 2020. A lokacin da yake Magana da jaridar Daily Trust a ranar Asabar, ya ce, “Ni maraya ne, mai yin noma kuma a yanzu ni kansila ne. A matsayina na maraya, na ɗauki noma da makaranta da muhimmanci, da harkar noma ne, na sami damar kula da mahaifiyata da kaina. Daga baya ne, na ci zabe don wakiltar garina. ”   Ya ce lokacin da mutane da yawa suka ji yana shirin auran mata biyu, sai suka yi mamaki ko shi ɗan sarki ne ko ɗan wani attajiri ne, amma an gaya musu cewa ni manomi ne. "A gaskiya na rike noma da matu...
Ji Abinda magidancinnan yayi bayan ya gano matarsa na Holewa da wani dansanda

Ji Abinda magidancinnan yayi bayan ya gano matarsa na Holewa da wani dansanda

Auratayya
Ma gidancin mai kimanin shekaru 44, a ranar litinin ya nemi da kotun sauraran kararraki dake legas, data kashe auransu bisa zargin daya kewa matarsa tana holewarta da wani jami'in dan sanda.   Wadda ake zargi mai suna Rashidat wacce suke da ya'ya' har biyu a tsakani, inda ya kara da cewa "Naduba wayarta wani lokaci inda naga irin kalaman batsa da take a WhatsApp ita da wani.   Ya bayyana ya sha yi mata magana amma tana uwar shegu dashi, gashi Sam bata shigar mutunci tamkar ba matar aure ba, na sha yi mata fada akan haka, amma dan abokaina suna shiga tsakanin mu ne, a cewar magidancin a lokacin da ya ke shaidawa kotu.   Itama ta tofa nata korafin a gaban alkali inda ta bayyana mijin nata a matsayin rigimamme, takara da cewa Mijin nata mai suna Ahmad yana yaw...

Ta roki babanta ya aurar da ita koma da waye

Uncategorized
Wannan wani gajeren hoton bidiyone da aka dauko daga cikin wani shirin fim din Hausa wanda ke nuna wata diya da tazo take rokon mahaifinta cewa itafa aure takeso koma waye a  bata zata zauna dashi, hoton ya dauki hankulan mutane sosai. Wasu sun rika tambayar cewa irin wannan yana faruwa da gaske kuwa? Kalla kaga yanda abin ya faru.

Ango da amaryarshi:Mahaifin amaryar yaki zuwa gurin shagalin dan ya nuna rashin amincewa da kashe kudi fiye da kima wajan shirya biki

Uncategorized
Wani malamin addinin musulunci me suna Farfesa Ishaq Akintola yaki zuwa gurin shagalin bikin diyarshi dan ya nuna rashin amincewarshi da kashe kudi fiye da kima da akeyi a wajaen bikin aure. Kamar yanda ya bayyanawa jaridar Punch yace yaki zuwa wajan shagalinne wanda akasaba yin anko da cinye-ciyen abinci tsakanin 'yan uwa da abokan ango da amarya ne bawai dan baya son diyarshi ko mijinta ba, yace yayi hakanne domin ya nuna rashin amincewarshi akan irin makudan kudin da babu gaira babu dalili mutum bashi da kwai yace sai yayi kuru yayi bikin kece raini, wani ma harda bashi zai ciwo bayan biki yazo ya shiga rigima. Yayi kira ga gwamnati data sanya haraji me tsauri akan duk wani biki da aka yanka Sa fiye da daya, ya yabi diyatshi inda yace tana da tarbiyya kuma irin diyar da ko wane u...

Banufe Umar ya auri inyamura A’ishat Obi

Uncategorized
A wannan lokacin da ake ganin kawunan kabilun kasarnan yana kara rarrabuwa wani abin birgewa da ban sha'awa ya faru inda wani Banufe da aka bayya sunanshi da Umar ya auri masoyiyarshi wadda inyamurace me suna A'isha Obi data fito daga jihar Imo. Saboda irin yanda suka birge mutane anyita sa musu albarka a shafukan sada zumunta da muhawara, muna muna musu fatan Allah ya yiwa wannan aure nasu albarka ya kuma kawo zuri'a ta garu.