fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Ayo Salami

Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito daga bangaren yan sanda ba>>Mai Shari’a Salami

Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito daga bangaren yan sanda ba>>Mai Shari’a Salami

Siyasa
Justice Ayo Salami, shugaban kwamitin da aka kafa domin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu, ya ba da shawarar cewa be kamata sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya fito daga rundunar ‘yan sanda. Ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Juma’a, bayan ya gabatar wa da Shugaba Muhammadu Buhari rahoton kwamitin da aka kafa don binciken zargin cin hanci da rashawa da Babban Lauyan nan kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, keyi akan shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.   A cewarsa, shugabannin hukumar EFCC hudu da suka gabata sun fito ne daga rundunar 'yan sanda ne, don haka ya kamata a ba da dama ga mutane daga wasu jami'an tsaro ko jami...
Na yi dana sanin shugabantar binciken Magu>>Mai Shari’a Ayo Salami

Na yi dana sanin shugabantar binciken Magu>>Mai Shari’a Ayo Salami

Siyasa, Uncategorized
Mai shari'a, Ayo Salami wanda tsohon shugaban babbar kotun gwamnatin tarayya ne ya bayyana cewa yayi nadamar shugabantar Binciken Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar, EFCC, Ibrahim Magu.   An hana 'yan Jarida shiga wajan da ake binciken inda kuma Magu ya fara kare kansa daga zarge-zargen da ake masa. Wasu lauyoyin magu 2, Zainab Abiola da Tosin Ajaoma sun bayyanawa Premium times cewa Mai Shari'a, Salami ya yi ta maimaita cewa yayi dana sanin shugabantar Binciken Magu.   Yace yana can gida zaune yana cin tuwo tun bayan da yayi rutaya amma yanzu ya zo ya saka kanshi a wannan bincike. Saidai da lauyoyin suka tambayeshi ko saboda an kasa samun Magu da laifine shiyasa yace haka?  Bai basu amsa ba.
An zargi shugaban Kwamitin dake Bincikar Magu, Ayo Salami da son ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus shiyasa baya so binciken ya kare

An zargi shugaban Kwamitin dake Bincikar Magu, Ayo Salami da son ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus shiyasa baya so binciken ya kare

Uncategorized
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin Mai shari'a Ayo Salami wanda shine ke jagorantar kwamitin dake binciken tsohon Mukaddashin shugaban hukumar EFCC,  Ibrahim Magu da ci gaba da neman a tsayawaitawa kwamitin nasa lokacin aiki saboda ya ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus da yake samu daga aikin. Kafar Sahara Reporters tace tuni shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita aikin kwamitin binciken da makwanni 6. Saidai tace maimakon tunanin aiki ne ya ma kwamitin yawa kwamitin yawa, maganar gaskiya itace son ci gaba da karbar Manyan alawus ne na shugaban kwamitin kamar yanda wata Majiya ta bayyana.   Majiyar ta yi zargin cewa a duk zaman da kwamitin yayi ana biyan mai shari'a Ayo Salami Naira Dubu 250 da kuwa sauran wasu alawus da ba'a son bayyanawa.   ...