fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Ayyukan yi

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Ayyukan Yi Miliyan Biyar>>Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Ayyukan Yi Miliyan Biyar>>Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo

Siyasa
Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo, ya ce tsarin farko na farfado da tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya za ta gudanar zai samar da ayyuka tare da hana ayyuka miliyan biyar durkushewa. Gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin ne domin magance tabarbarewar tattalin arzikin kasa ne sakamakon annobar cutar korona. Ministan ya ce akwai tsari a kasa da zai hana durkushewar akalla ayyukan yan Najeriya miliyan daya da dubu dari hudu, wanda kashi 40 kananan sana’oin mata ne da nakasassu. Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Mai taimaka masa a harkokin yada labarai, Julius Toba-Jegede, ya sanya wa hannu ranar alhamis. Ministan ya kara da cewar wannan wani yunkuri ne da ma’aikatarsa ke yi na ganin an yi nasara a shirin gwamnatin tarayya na...