
A yau za’a kara gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal a kotu bisa zargin Almundahanar Miliyan 500
Hukumar hana rashawa da cin hanci, EFCC a yau zata kara gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da wasu 6 a kotu bisa zargin almubazzaranci da Naira Miliyan 544 na kudin sare ciyawa.
Wannan ne karo na 2 da za'a kara gurfanar da wanda ake zargi din biyo bayan gurfanarwar farko da aka musu a watan Fabrairu na shekarar 2019.
EFCC ta zargi Lawal da bada kwangilar yanke ciyawar ga kamfanoni wanda yake da hannu jari a ciki amma ya karyata hakan.