Friday, May 29
Shadow

Tag: Babagana Umara Zulum

Hotuna:Yanda Janar Buratai ya jewa Gwamnan Borno Gaisuwar Sallah da kuma yanda yayi Bikin Sallah da Sojoji

Hotuna:Yanda Janar Buratai ya jewa Gwamnan Borno Gaisuwar Sallah da kuma yanda yayi Bikin Sallah da Sojoji

Tsaro
Shugaban Sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya jewa gwamnan jihar Borno,  Babagana Umara Zulum Gaisuwar Sallah a ofishinsa. Yayin ziyarar, Buratai ya bayyana Zulum a matsayin me baiwa hukumar sojin goyon baya yanda ya kamata.   A martaninsa, Zulum ya bayyana cewa, Zai ci gaba da baiwa Sojojin goyon baya kuma duk da cewa an dan samu rashin fahimta amma a koda yaushe sojojin na a ransa.     Janar Buratai ya je Maimalari inda yayi bikin Sallah da sojoji, da kansa ya rika zuba musu abincin Sallaha a kwanukansu.
Gwamna Zulum ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin Borno saidai ya iske shuwagabannin kananan hukumomin basa bakin aiki

Gwamna Zulum ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin Borno saidai ya iske shuwagabannin kananan hukumomin basa bakin aiki

Siyasa
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin jihar 6 inda ya iske shuwagabannin kananan hukomomin basa bakin aiki.   Sanarwar ta bayyana cewa hakan ya farune duk da cewa sati 2 da suka gabata gwamnan ya bada umarnin a dawo a ci gaba da aiki. Yace dama tun kamun zuwan Coronavirus/COVID-19 ya samu rahotannin cewa shuwagabannin kananan hukumomin Askira-Uba, Bama, Gwoza, Damboa da Chibok basa zuwa wajan aiki, a Maiduguri suke zaune sai idan za'a kaiwa kananan hukumomin kasonsu ko kuma zai kai ziyarane suke zuwa.   Yace yayi gargadi akan hakan inda ya bukaci shuwagabannin kananan hukumomin su rika kasancewa a kananan hukumominsu dan mutane su san ana yi dasu amma ga dukkan alamu basu ji gargadin nashi ba, yace dan...
Yanzu-Yanzu: Gwamna Zulum zai gina Ofishi a Garin Auno inda zai rika gudanar da ayyukansa dan maganin yawa kaiwa garin harin da Boko Haram suke

Yanzu-Yanzu: Gwamna Zulum zai gina Ofishi a Garin Auno inda zai rika gudanar da ayyukansa dan maganin yawa kaiwa garin harin da Boko Haram suke

Siyasa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya bada umarnin a gina masa ofishi a garin Auno dake tsakanin Maiduguri da Damataturu dan yayi maganin yawan kaiwa garin hari da Boko Haram suke.   Gwamnan ya bayyana hakane a ziyarar daya kai garin a yau inda ya kaddamar da aikin gina wasu gidaje 500.   Yace garin Auno yana da matukar muhimmanci saboda da yawa 'yan Maiduguri sukan je garin du yi noma kuma lalata garin Auno kamar lalata birnin Maiduguri ne, Gwamna Zulum wanda yanzu haka ofishi 2 yake amfani dashi, dana gidan gwamnati dana sakatariyar jihar dan tabbatar da hana zuwa aiki a makare da yin aiki yanda ya kamata tsakanin ma'aikata na son ginda Ofishi na 3.   Gwamnan zai kuma yi amfani da sabon ofishin nashi wajan ganawa da jama'ar gari...
Karatun Allo Al’ada Ce Ta Al’ummar Jihar Borno Don Haka Ba Zan Iya Hanawa Ba>>Gwamna Zulum

Karatun Allo Al’ada Ce Ta Al’ummar Jihar Borno Don Haka Ba Zan Iya Hanawa Ba>>Gwamna Zulum

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ba zai iya raba jihar Borno da karatun Allo ba, kuma ba zai kulle makarantun Allo ba.     Gwamnan ya kara da cewa; gwamnatin Borno za ta hana Almajirai yawo a kan hanya da kuma mayar da almajiran da aka kawo su daga nesa gaban iyayensu, sannan gwamnati za ta taimakawa Malaman Makarantun Allo gwargwadon iko domin su kula da Almajiran dake gabansu. Rariya
Gwamnatin Borno za ta hukunta limamai 3 saboda bijirewa dokar hana cinkoso

Gwamnatin Borno za ta hukunta limamai 3 saboda bijirewa dokar hana cinkoso

Uncategorized
Gwamnatin Jihar Borno dake Najeriya tace babu tantama za ta hukunta wasu limamai 3 da suka bijirewa dokar hana cinkoson jama’a wajen gudanar da sallar Juma’a.     Kwamishinan yada labaran jihar Babakura Abba-Jato, yace sun gano masallatan guda 3 ne, a lokacin da suke zagaya garin Maiduguri domin tabbatar da ana aiwatar da dokar hana cinkoson, ganin yadda coronavirus ta kama mutane 12 a Jihar.     Aba-Jato yace gwamnati ta fusata dangane da lamarin, kuma ta gabatar da limaman gaban Shehun Borno. Ranar alhamis gwamnatin Borno ta yi shelar kafa dokar hana zirga-zirga zuwa ciki da wajenta, da kuma haramta tarukan addini, bukukuwa da kuma a ababen hawa, domin dakile yaduwar annobar coronavirus da ta bulla a jihohin Najeriya 27.
Wadannan hotunan bana gurin da muka ware dan kula da masu cutar Coronavirus/COVID-19 bane>>Gwanan Borno

Wadannan hotunan bana gurin da muka ware dan kula da masu cutar Coronavirus/COVID-19 bane>>Gwanan Borno

Uncategorized
Gwamnan jihar Borno,  Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa hotunan nan da suka yawo a shafuka  sada zumunta bana wajan da suka shirya bane dan tarar cutar Coronavirus/COVID-19.   Yace gurin kula da cutar Koda ne dake jihar ta Borno ba gurin shirin tarbar cutar Coronavirus/COVID-19 ba. https://twitter.com/ProfZulum/status/1242502193833484289?s=19   Zulum yace suna daukar matakan kariyane har yanzu