fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Tag: Babagana Umara Zulum

Zulum Ya Fi Ni, Ta Kowane Fanni>>Tshohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima

Zulum Ya Fi Ni, Ta Kowane Fanni>>Tshohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima

Siyasa
Sanata Kashim Shettima mai wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dokoki ta kasa ya tabbatar da cewa zabar Gwamna Babagana Zulum a matsayin wanda zai gaje shi ba don wasu dalilai na kashin kansa ba amma don maslahar jihar ta Borno ne. Ya yi nuni da cewa Farfesa Zulum 'ya fi shi a duk wasu bangarori.' Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata makala a wajen taron laccar Jama'a da Hadin gwiwar Kungiyoyin Matasa suka shirya a Birnin Kebbi tare da taken: "Cigaban Matasa da Jagoranci." Ya bayyana cewa ya tsallake matsaloli da yawa har ya kai ga ya zabi wanda zai gaje shi, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda kuma ya bayyana a matsayin amintaccen dan siyasa. Tsohon Gwamnan ya shawarci shuwagabanni da su fahimci cewa shugabanci ya kasance ama...
Gwamna Zulum ya dauki Nauyin Karatun ‘ya’yan ‘yan Sakai

Gwamna Zulum ya dauki Nauyin Karatun ‘ya’yan ‘yan Sakai

Siyasa
Gwamnatin Jihar Borno ta ɗauki nauyin karatun 'ya'yan mayaƙan sa-kai da aka fi sani da Civilian JTF waɗanda suka rasa rayukansu yayin yaƙi da ƙungiyar Boko Haram. Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da hakan a Maiduguri, babban birnin jihar a yau Laraba yayin wani taro da ya tara dakarun sa-kai da ke taya sojoji yaƙi da 'yan bindiga Borno. Kazalika gwamnan ya amince da bai wa matan waɗanda aka kashe ɗin naira 50,000 kowaccensu. Taron ya gudana ne a Jami'ar Jihar Borno. Wata sanarwa da sashen yaɗa labaran gwamnatin Borno ya fitar ta ce gwamnan ya bai wa kowane mutum ɗaya naira 20,000 na mutum 9,000 da suka halarci taron. Haka nan, an bai wa kowannensu buhun shinkafa ɗaya da kwalin taliya ɗaya da galan ɗin man girki. Yaƙin Boko Haram wanda aka shafe tsawon shekara 10 ana yi, ya yi
Gwamna Zulum ya baiwa jamian tsaro umarnin Murkushe duk wata zanga-zanga a jihar Borno

Gwamna Zulum ya baiwa jamian tsaro umarnin Murkushe duk wata zanga-zanga a jihar Borno

Tsaro
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya baiwa jami'an tsaro a jihar Umarnin su Murkushe duk wani yunkuri na zanga-zanga a jihar.   Gwamnan ya bayyana cewa zanga-zanga a shwkarar 2009 kan kin amincewa da saka hular kwano ce ta haifar da Boko Haram. Yace dan haka ba zasu lamunci duk wata zanga-zangar da zata kawo musu koma bayan ci gaban tsaro ba. Yace ya samu bayanan sirri na cewa wasu da aka dauki nauyinsu na son yin zanga-zanga dan nuna rashin jin dadi kan ayyukan soji.   Governor Zulum, who commended the Borno youth for “not participating in the meaningless protest that was hijacked by hoodlums” said his administration would not tolerate any protest that would threaten the fragile security in the state. The governor said he has instructed the security
Zulum ya raba miliyan N65 a tsakanin zawarawa da wasu mutane a Rann

Zulum ya raba miliyan N65 a tsakanin zawarawa da wasu mutane a Rann

Siyasa
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Asabar ya tashi da tsabar kudi Naira miliyan 65 zuwa Rann, hedikwatar Kala-Balge, da ke tsakiyar jihar, don tsananin bukatun jin kai. Ziyarar ita ce ta biyar da Zulum ya taba kai wa Kala-Balge ziyara tun lokacin da ya hau karagar mulki a watan Mayun 2019. Rann, hedikwatar Kala-Balge, an katse shi daga sauran sassan Borno saboda wata ambaliyar ruwa da ta tashi daga madatsar ruwa daga Afirka ta Tsakiya, da hana su damar zuwa gonakinsu, wadanda suma ambaliyar ta shanye su. Mazauna kauyen galibi suna sayen kayan abinci ne daga kauyen da ke kan iyaka a Jamhuriyar Kamaru mai makwabtaka, don rayuwa. Zulum, yayin tafiyar Asabar din, ya kula da rabar da tsabar kudi har Naira miliyan 65 ga iyalai zawarawa 8,000 da wasu mazauna marasa karfi a Ra...
Gwamna Zulum ya ciri tuta tsakanin Gwamnoni, yana ta shan Yabo saboda ya rabawa mutanensa tallafin Coronavirus/COVID-19 yanda ya kamata

Gwamna Zulum ya ciri tuta tsakanin Gwamnoni, yana ta shan Yabo saboda ya rabawa mutanensa tallafin Coronavirus/COVID-19 yanda ya kamata

Siyasa
A yayin da ake ta samun matsalar fasa rumbunan ajiyar tallafin Coronavirus/COVID-19 a jihohin Najeriya, mutane na ta yabawa Gwamnan jihar, Borno, Babagana Umara Zulum.   A lokuta da dama an sha ganin Gwamna Zulum yana rabon kudi da kuma kayan Abinci, ba indomi 1 ba ko kwano daya ba, a'a buhu-buhu da kwalayen Indomi za'a baiwa mutum daya.   Gwamnan sai shan Yabo yake daga sassa daban-daban na kasarnan.   Hakanan a kudancin Najeriya ma, Gwamna Hope Uzodinma ma na jihar Imo shima yana ta shan Yabo saboda rabawa mutane Abincin tallafin Coronavirus/COVID-19 din yanda ya kamata.   https://twitter.com/adamm_mo/status/1320028343102808068?s=19 https://twitter.com/Abdulrazaq_Doga/status/1320064192909631488?s=19 https://twitter.com/AM_Saleeem/status/1...
Hotuna:Bayan da Gwamna Zulum ya mayar da Mazauna Baga garinsu, Harkoki sun fara dawowa daidai a Garin

Hotuna:Bayan da Gwamna Zulum ya mayar da Mazauna Baga garinsu, Harkoki sun fara dawowa daidai a Garin

Siyasa
A kwanakin bayane gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da mayar da mutane  Baga garinsu bayan kwashe tsawon lokaci suna zaune a matsugunan 'yan gudun Hijira.   Gwamnan ya sha nanata cewa, gwamnati ba zata iya ci gaba da ciyar da mazauna sansanonin Gudun hijirar ba dolene a mayar dasu gidajensu su nemi na kansu.   Wadannan hotunan yanda harkokin rayuwa suka fara dawowa daidai ne Baga, bayan komawar mutane.   https://twitter.com/Habuhk4/status/1319948524558176256?s=19   This is #Baga life's gradually taking shape. It's only when U leave an empty space that other things move to fill it. We cant allow our reclaimed towns to stay empty anymore while BH, Rodents etc claim them. Kudos to @ProfZulum's resettlement of IDPs back to their ance
Gwamna Zulum ya nemi jama’ar Borno su tashi da Azumi gobe dan addu’ar kawo karshen Boko Haram

Gwamna Zulum ya nemi jama’ar Borno su tashi da Azumi gobe dan addu’ar kawo karshen Boko Haram

Tsaro
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya umarci al'ummar jihar da su ɗauki azumi a gobe Litinin domin yin addu'o'in kawo ƙarshen rikicin Boko Haram. Gwamnan ya ayyana Litinin a matsayin rana ta biyu ta azumi a faɗin jihar ne ranar Asabar yayin da yake jawabi a wurin wani taron masu ruwa da tsaki da ya jagoranta a Maiduguri, babban birnin jihar. Zulum ya ce ɗaya daga cikin hanyoyin da mutane za su taimaka a yaƙi da Boko Haram ita ce, kar su shiga ƙungiyoyin 'yan bindiga sannan su riƙa taimaka wa sojoji da bayanai da kuma yin addu'o'i. "Bisa wannan yunƙruin ne na kirawo taro da Mai Alfarma Shehun Borno da Babban Limami da limaman masallatan Juma'a da shugabannin Kiristoci muka tattauna," in ji shi. "Biyo bayan wannan tattaunawa, na ayyana Litinin, 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar
Gwamna Zulum ya baiwa wanda harin Boko Haram ya shafa tallafin kudi da kayan gini

Gwamna Zulum ya baiwa wanda harin Boko Haram ya shafa tallafin kudi da kayan gini

Siyasa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana baiwa 'yan Gudun Hijira da Boko Haram suka raba da Muhallansu su 1,111 tallafin kayan gini da kuma kudi.   Gwamnan ya bayar da wannan tallafine a Yawuri dake karamar hukumar Jere ta jihar. Yace sun bayar da tallafinne dan mutane su samu su sake gina gidajensu dan su koma garuruwansu da zama su kuma samu sana'a.   Gwamnan ya baiwa mutanen tabbacin gina makarantu da Asibitoci dan amfaninsu.
ZABEN 2023: Zulum Ne Ya Kamata Ya Shugabanci Nijeriya>>Sheikh Gadon Ƙaya

ZABEN 2023: Zulum Ne Ya Kamata Ya Shugabanci Nijeriya>>Sheikh Gadon Ƙaya

Siyasa
Babban malamin addinin musulunci, Dr. Abdallah Usman Gadon-Kaya, ya yi magana game da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum. A wajen wani karatu da Abdallah Usman Gadon-Kaya ya ke yi, ya lissafo alheran gwamnan Borno, ya ce irinsa su ka dace su rike mulkin Najeriya.   Malamin ya ke cewa a wannan marra, babu gwamna da aka yi na kirki irin Farfesa Umara Zulum. Ya ce: “Allah ya saka wa gwamnan Borno da alheri, a cikin gwamnonin Arewa ko na Najeriya wadanda mu ka sani, Allah bai yi wani gwamna irinsa ba a kwanan nan." “Alheransa sun bayyana, mutuncinsa ya bayyana, tsoron Allah na sa ya bayyana.” Inji Shehin. Ya ce akwai wani na-kusa da gwamnan da ya shaida masa duk ranar Litinin da Alhamis, sai Zulum ya yi azumin nafila, wanda ya na cikin manyan ibadu nafila.