fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Tag: Babagana Umara Zulum

Zulum Ya Zargi Cewa Akwai Wata Makarkashiya, Ya Bukaci Shugaba Buhari Yayi Bucike Don Sanin Gaskiya

Zulum Ya Zargi Cewa Akwai Wata Makarkashiya, Ya Bukaci Shugaba Buhari Yayi Bucike Don Sanin Gaskiya

Tsaro
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya nace cewa akwai makarkashiya a cikin tsarin gwamnati da ba zai bari a kawo karshen ta'addanci ba a Arewa maso Gabas. Ya fadi hakan ne a ranar Lahadin nan lokacin da ya gana da Gwamnonin jihohin Kebbi da Jigawa, Atiku Bagudu da Badaru Abubakar, wadanda suka kai masa ziyara kan harin da aka kai kwanan nan a Baga - wani gari a Borno. Gwamna Zulum ya yi imanin wasu abubuwan suna kokarin kawo cikas ga kokarin da gwamnati keyi na kawo karshen ta'adancin kuma shugaban na bukatar sanin gaskiya. Ya jaddada bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba matsalar tsaro a yankin da sosai, don tabbatar da kokarin gwamnatin sa bai zamo a banza ba. Taron wanda ya samu halartar Mataimakin Gwamnan jihar, Umar Kadafur, wanda aka yi a Gidan Gwamnat...
Gwamna Zulum Ya Ba Da Shanu 4 Ga Yan Bautar Kasa Yayin Bikin Sallah

Gwamna Zulum Ya Ba Da Shanu 4 Ga Yan Bautar Kasa Yayin Bikin Sallah

Siyasa
Gwamna Babagana Zulum ya ba da shanu guda hudu ga membobin kungiyar yan bautar kasa da ke aiki a jihar Borno domin bikin Eid-el-Kabir. Da yake mika shanun ga wakilan mambobin kungiyar a ranar Asabar a cikin garin Maiduguri, Zulum ya ce wannan shi ne tabbatar da cewa wadanda ba su yi tafiya gida zuwa sallah ba kuma suna da abin da za su yi bikin. Zulum, wanda babban jami'in hukumar kula da yan bautar kasa (NYSC) ya wakilta a jihar, Mista Christopher Godwin-Akaba, ya yaba da gudummawar da mambobin kungiyar ke bayarwa ga ci gaban jihar. Yayin da ya tabbatar wa mambobin kungiyar goyon bayansa a koyaushe, gwamnan ya ce hakan zai ci gaba da sadaukar da kai don jin dadin su, musamman biyan su hakkokin su. Ya bukace su da su ci gaba da yin addu’a don samun hadin kai da dawwamamme
Ban Girgiza Ba>>Gwamnan Zulum

Ban Girgiza Ba>>Gwamnan Zulum

Tsaro
Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya bada tabbacin cewa yana cikin koshin lafiya duk da harin Baga da aka kaiwa ayarin sa. Zulum ya ce bai girgiza ba kuma zai ci gaba da aiwatar da ayyukansa ba tare da tsoro ba. Ya yi magana da DAILY POST a ranar Asabar ta hannun mai magana da yawun sa, Isa Gusau. “Gwamnan ba shi da tsorata ba, kuma bai girgiza ba. Kuma kyautatawa rayuwar mutanen Borno shine babban fifikonsa kuma zai ci gaba da aiki yadda ya dace domin su ”, in ji Gusau. Zulum ya godewa dukkan 'yan Najeriya saboda hadin kai da addu'o'in su. Ya yi kira ga 'yan kasa da su kasance takatsantsan kuma su ci gaba da bin duk kaidojin kare yaduwar cutar corona.
Matsalar Boko Haram ba laifin Buhari ko Buratai bane>>Gwamna Zulum

Matsalar Boko Haram ba laifin Buhari ko Buratai bane>>Gwamna Zulum

Tsaro
A jiyane gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gamu da harin Boko Haram a kan hanyarsa ta zuwa garin Baga.   Saidai kamin ya tafi garin sojoji sun bashi tabbacin cewa sun kori Mayakan Boko Haram daga garin. Wannan ne yasa gwamnan ya koma wajan sojojin ya caccakesu kan wannan lamari da ya faru. Yace akwai tulin Sojoji a Monguno kuma akwaisu a inda tsakaninsu da Baga babu nisa yace amma sun kasa shawo kan matsalar. Yace Matsalar Boko Haram ba wai laifin shugaba Buhari ko Buratai bane, yace matsalar daga masu bayar da umarnin ya da za'a gudanar da yakinne.   Gwamnan yayi zargin cewa akwai zagon kasa a yaki da Boko Haram,  Kamar yanda The Cable ta ruwaito kuma yace zasu baiwa sojojin Lokaci amma idan suka kasa zai dauki hayar mafarauta.
Na Gamsu Da Salon Mulkinka, Buhari Ga Gwamna Zulum

Na Gamsu Da Salon Mulkinka, Buhari Ga Gwamna Zulum

Siyasa
Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin saro, Manjo Janar Babagana Monguno ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Zulum a Maiduguri ranar Alhamis.   Janar Monguno ya kasance a cikin Maiduguri don yin ta'aziyya ga Gwamnati da jama'ar jihar Borno game da mummunan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a kwanakin baya, inda aka kashe mutane da dama. Monguno ya samu rakiyar ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, Shugaban Hukumar Leken Asiri na kasa, Shugaban kwamiti mai kula da ayyukan soji na majalisar dattijai, Sen. Mohamed Ali Ndume, Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan ayyuka na musamman, Sen. Yusuf A. Yusuf, da Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan NEDC Hon Hadiza Bukar Abba.   "Ya maigirma Gwamna, Shugaban kasa ya nemi d...
Sai Nijeriya Ta Kara Sojoji Kafin Galaba Kan Boko Haram>>Zulum

Sai Nijeriya Ta Kara Sojoji Kafin Galaba Kan Boko Haram>>Zulum

Tsaro
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Litinin ya bayyana wasu daga cikin dalilin da ya sa har yanzu Gwamnatin Tarayya hadi da rundunar sojoji, su ka kasa cin nasarar kawo karshen Boko Haram din da ta dauki dogon lokaci a kasar, inda ya ce sai Nijeriya ta kara yawan sojojin da ta ke da su kafin iya yin galaba kan kungiyar Boko Haram. Gwamna Zulum ya yi wannan furucin ne a lokacin da tawagar zauren majalisar dattijai ta kai ziyara jihar, domin yi wa al’umma jaje da ta’aziyyar hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a garuruwa daban-daban a jihar ta Borno. Tawagar sanatocin, a karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, hadi da mai tsawatarwa, Sanata Orji Kalu, sun ziyarci birnin Maiduguri ne, don nuna alhininsu ga al’umma
Nijeriya Na Neman Karin Sojoji Domin Tunkarar Boko Haram, Inji Gwamna Zulum

Nijeriya Na Neman Karin Sojoji Domin Tunkarar Boko Haram, Inji Gwamna Zulum

Tsaro
Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya yi tsokaci kan wasu muhimman dalilai da suka sa har yanzu Nijeriya ta kasa gamawa da Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas.   Zulum ya fadi haka ne a yayin da yake maraba da tawagar sanatocin da suka zo yi masa jajen kisan mutanen da Boko Haram suka yi a ‘Yan kwanakinan a jihar. Bulaliyar majalisar, Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima da wasu sanatoci biyu dake wakiltan shiyyoyi a jihar Barno na daga cikin tawagar da suka ziyarci gwamna Zulum.   A bayanin da ya yi gwamna Zulum ya ce rashin isassun sojoji na daga cikin matsalolin dake kawo wa Najeriya cikas wajen gamawa da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.   Sannan yayi kira ga sanatocin su binciki rashin kudi da sojojin ke kuka da su
Gwamna Zulum Ya Nuna Kin Aminincewa Game Da Wasu Bulalluka Marasa Kyau Na Rukunin Ginin Gidaje 500 A Garin Auno

Gwamna Zulum Ya Nuna Kin Aminincewa Game Da Wasu Bulalluka Marasa Kyau Na Rukunin Ginin Gidaje 500 A Garin Auno

Siyasa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Asabar ya ba da umarnin a sauya wadansu bulalluka marasa inganci a wurin gina rukunin gidaje 500 a garin Auno.     Auno gari ne, wanda ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno.   Gwamnan baya ga rukunin gidaje 500 da ke Auno, ya kuma duba aikin gina masaukin baki a Jami’ar Jihar Borno da kuma kammala aikin Makarantar Sakandaren Moramti, duk a cikin ran gadin da yi a yau asabar.     Gwamna Zulum ya dawo Maiduguri ranar Juma’a bayan halartar wani taro da Shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, ya gana da ministocin aikin gona, kudi, harkokin jin kai da kuma Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira. Gwamnan ya kasance a cikin dukkan ayyukan da
Shugaba Buhari ya gana da gwamna Zulum

Shugaba Buhari ya gana da gwamna Zulum

Uncategorized
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a fadarshi a yau, Litinin.   Ganawar tasu ta kasance ta sirri daidai an yi tsammanin cewa Gwamna Zulum ya baiwa shugaban kasar bayanine kan hare-haren da Boko Haram suka kai jihar. A bayabayannan Boko Haram sun kai Hari Gubio inda suka kashe mutane akalla 81 sannan kuma sun kai hari Monguno da yankin Gubio a karo na biyu.
Ayyukan raya kasa 326 gwamna zulum yawa Barnawa cikin shekara daya data gabata

Ayyukan raya kasa 326 gwamna zulum yawa Barnawa cikin shekara daya data gabata

Siyasa
Sakataren gwamnatin jihar Borno, Alhaji Usman Jidda ya bayyana cewa, gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum yayi ayyikan raya kasa 326 a cikin shekara 1 data gabata.   Ya kuma kara da cewa akwai tsare-tsare 49 da gwamnan ay aikwatar a tsawon shekarar. Yace wasu daga cikin ayyukan da gwamnan yayin sun hada da ginin gidaje 6,544 a kananan hukumomi 12 na jihar dan mutanen dake gudun hijira su koma garuruwansu.   Akwai kuma fanfan tuka-tuka 133, da guraren bada kulawar lafiya na matakin farko guda 37 a kananan hukumomi 17, da kuma wasu sabbin tituna da wanda ake gyarawa gida 30 sannan ga gadar sama ta farko da ake kan ginawa a jihar.   Jidda ya kuma ce akwai motoci 300 na sintiri da jihar ta siya ta baiwa jami'an tsaro.   Kamfanin dillancin labar...