fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Tag: Babagana Umara

Mu ne muka kaiwa Gwamna Zulum hari>>IS

Mu ne muka kaiwa Gwamna Zulum hari>>IS

Tsaro
Wasu da ake zargi masu iƙirarin jihadi ne sun sake kai wa tawagar gwamnan Borno Babagana Zulum hari dai-dai lokacin da suke komawa Maiduguri, babban birnin jihar. Gwamnan ya tsira da ga hari na ranar Lahadi sannan ba a samu asarar rai ba. Babu tabbaci kan ko gwamnan yana cikin tawagar. Harin dai ya faru ne kusan sa'a 48 bayan da masu ta da ƙayar bayan suka afkawa tawagar gwamnan a yankin Baga inda kimanin mutum 30 suka mutu a harin - har da sojoji da ƴan sanda. Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai harin. Gwamna Zulum ya kai ziyara yankin Baga a ƙoƙarin da ake na maido da dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita matsugunansu. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar ya yi Allah ...