
Da Duminsa:Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan Legas in ya bashi Rahoto kan yanda za’a sake gina Legas din
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na ganawa da gwamnan Legas a fadarsa dake Abuja.
Hadimin shugaban, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a ta shafinsa na sada zumunta, Sadai bai bada cikakken bayani kan ganawar shuwagabannin ba.
Amma Hutudole ya fahim ci cewa Gwamnan Legas din ya mikawa shugaba Buhari Rahoto ne kan yanda za'a sake gina Birnin Legas, wanda ba ya rasa nasaba da Asarar da Birnin ya tafka a yayin zanga-zangar SARS.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1347164726044864513?s=19
PHOTOS: President Muhammadu Buhari receives in audience Lagos State Governor, H.E. Babajide Sanwoolu this afternoon, at the State House, Abuja.