
Kotun Shari’ar Musulunci Ta Gayyaci Baban Chinedu Kan Yi Wa Afakallah Kazafi
Sakamakon maganganun da Haruna Yusuf (Baban Chinedu) yayi wadanda a cikinsu yake zargin Ismael Na'Abba Afakallah da cinye kudaden marayu, hakan ya sa shi Afakallah ya garzaya zuwa kotun Musulunci domin neman a fito da gaskiyar maganar dashi Baban Chinedu yayi akansa.
Bayan da kotun wadda take a unguwar Hausawa a Filin Hocky ta saurari korafi daga mai kara, sai ta saka ranar 1 ga watan 4 na shekarar 2020 domin fara sauraren shariar.
Tuni kotu ta turawa da Baban Chinedu takardar gayyata zuwa ofis dinsa dake Kano.