
“Gida zan koma ba zan tsaya takarar shugabancin Najeriya ba”>> Fashola
Ministan gidaje Babatunde Fashola ya bayyana cewa shi ba zai nemi takarar shugabanci Najeriya ba a shekarar 2023.
Tsohon gwamnan jihar Legas din ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai, bayan wasu kungiyoyi sun bukaci shi daya tsaya takarar.
Amma shi ya bayyana cewa gida zai koma da zarar ya bar ofishinsa kuma yana yiwa masu neman takarar shugabancin fatan nasara.