fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Babbar Sallah

Babbar Sallah: ‘Yin amfani da tayoyi don babbake gashin dabba yana haifar da cutar kansa – A cewar Masana

Babbar Sallah: ‘Yin amfani da tayoyi don babbake gashin dabba yana haifar da cutar kansa – A cewar Masana

Kiwon Lafiya
Likitocin dabbobi a jihar Kano sun gargadi masu yin amfani da tayoyi wajan babbake kai da kafa harda fatar jikin dabbobi, bayan an yanka dabba, na iya haifar da cutar Kansa. Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar reshen jihar Kano, NVMA Junaidu Yakubu Muhammad ya fitar a ranar Talata. Muhammad wanda ya ce amfani da tayoyin zai iya haifar da cutar kansa, inda ya bukaci musulmai da suyi amfani da itace ko tukunyar gas a maimakon tayoyi. Ya kuma shawarci masu yin layya da su tabbata sun samu lafiyayun dabbobi, a yayin da za suyi layya, inda ya kuma shawarci mutane da su kauce yin amfani da dabbar da ke nuna alamon rashin lafiya ko makamantan hakan.