
Gwamna Badaru na jihar Jigawa ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2021
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya sanya hannu kan kasafin kudin jihar da ya ta samma Naira biliyan 156.588.
Daily Independent ta ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Jigawa ta zartar da kasafin kudin inda ya zama doka batare da jan kafa ba.
Gwamna Badaru, ya yabawa majalisar dokokin jihar bisa kokarin da su kai wajan zartar da kudiran ba tare da an kai ruwa rana ba.
Hakanan Gwamnan Ya bada tabbacin cewa kasafin zai fara aiki daga watan Janairun sabuwar shekaerar 2021 domin inganta rayuwar ‘yan kasa.