
Hotuna: Gwamnatin Jihar Kano ta mayarwa jihar Kebbi Al’majirai 61
Gwamnatin Jihar kano ta maida al'majirai 61 zuwa jahar su ta asali, hakan na zuwa ne a bisa kokarin da Jahohin Arewacin Najeriya ke yi don magance harkar al'majirci a fadin yankin Arewa.
An mayar da al'majiran ne tare da Malaman su, inda aka karbi al'majiran a Birnin Kebbi sansanin 'yan gudun hijira dake Kalgo a ranar Juma'a 22 ga watan Mayu.
Haka zalika gwamnan jihar Bagudu ya shaida da Lamarin.