
Gwamna Bagudu na jihar Kebbi ya jajan tawa Wamakko game da rasuwar ɗan wansa
Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a ranar Litinin, ya yi wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ta'aziyyar rasuwar dan uwansa, Dakta Bello Magatakarda Wamakko.
Gwamna Bagudu ya kai ziyarar ta’aziyar ne zuwa Garin Wamkko dake Sakkwato, tare da rakiyar Mai Kula da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Haruna Abubakar Maitandu.
Gwamnan ya ce ya kadu lokacin da ya samu labarin mutuwar Dakta Bello Wamakko.
Hakanan Gwamanan yayi addu'ar fatan rahama ga mamacin.
Dayake jawabi tsohon gwamnan jihar Sokoto ya godewa gwamana Bagudu bisa karamacin da ya nuna masa.