fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Bakasi

‘Yan ta’addar Bakasi sun kashe Inspector din ‘yansanda

‘Yan ta’addar Bakasi sun kashe Inspector din ‘yansanda

Tsaro
Wasu 'yan ta'adda da ake tunin na Bakasi ne suka sake bulla sun kaiwa jami'an 'yansanda hari a wani shinke da suka kafa inda suka kashe Inspector daga ciki wanda ba'a bayyana sunansa ba.   Sun kuma kwace bindigu guda 2 na 'yansandan inda suka gudu dasu. Wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa, maharan sun zo da yawa inda suka mamayi 'Yansandan.   Shugaban karamar hukumar, Amboni Nakanda Iyadim ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun yi zama da jami'an tsaro kuma nan bada dadewa ba za'a bincika domin gwato bindigun da aka kwace da kuma kama wanda su ka yi aika-aikar.