
“Neman kujerar shugaban kasa ba karamin aiki bane, kuma don Bauchi na tsaya takarar”>>Gwamna Bala Muhammad
Gwamnan jihar Bauchi mai neman kujerar shugaban kasa a PDP, Bala Muhammad ya bayyana cewa neman takarar shugaban kasa ba karamin aiki bane a matsayin shi na gwamna.
Muhammad ya bayyana hakan ne a ranar juma'a a wata liyafar shan ruwa daya hada inda ya gayyaci 'yan kwadago da manyan manema labarai da 'yan kasuwa.
Yayin daya basu hakuri cewa wannan shekarar bai yi masu abinda yayi a bara ba, amma dalili shine yana fafutukar neman takarar shugaban kasa ne kuma don cigaba su yake neman kujerar.