Masu garkuwa da mutane sun sace dan uwan gwamnan Bauchi
Masu garkuwa da mutane sun sace dan uwan gwamnan Bauchi.
An tabbatar da sace babban dan uwan gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed a yammacin yau.
A cewar wata majiya dake da kusanci dashi, dan uwan nasa mai suna Adamu Mohammed Duguri, an kama shi ne da misalin karfe 7:30 na daren Laraba a Anguwar Jaki da ke cikin garin Bauchi.