fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Bale

Tottenham 3-1 Stoke City: Yayin da Bale yaci kwallo kuma Tottenham ta cancanci buga wasannin kusa da karshe na gasar kofin Carabao

Tottenham 3-1 Stoke City: Yayin da Bale yaci kwallo kuma Tottenham ta cancanci buga wasannin kusa da karshe na gasar kofin Carabao

Wasanni
Kungiyar Tottenham tayi nasarar kai wasannin kusa da karshe na gasar kofin Carabao bayan ta lallasa Stoke City daci 3-1 ta hannun Gareth Bale da Harry Kane da kuma Ben Davies wanda yaci kwallon shi ta farko a kungiyar tun shelara 2017. Manajan Tottenham, Jose Mourinho ya kalubalanci dan wasan shi Dele Alli a wasan, sakamakon sakacin shine yasa Stoke City taci kwallo guda, yayin da yake cewa Alli yana kawowa kungiyar Spurs matsala kuma kamata yayi ace yana taimakawa wurin cin cin kwallaye ba wai ya ringa kawowa kungiyar shi matsala ba. Mourinho yana yin nasarar lashe wannan kofin na Carabao idan har ya kai wasannin kusa da karshe, kuma kocin ya kara da cewa idan har suna so su lashe kofin to zai sun yi nasarar cin wasannin su na gaba guda biyu masu wahala.