fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Bam

Yan Sanda Sun Gano Wani Abun Fashewa Mai Kama da Bam a Jihar Kano

Yan Sanda Sun Gano Wani Abun Fashewa Mai Kama da Bam a Jihar Kano

Tsaro
An samu fargaba a ranar Juma'a a garin Jogana, wani yanki da ke tazarar kilomita kaɗan daga birnin Kano, biyo bayan gano wani abun fashewa a Aujirawa Alkali, wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar. Masu motocin da ke bin hanyar Hadejia dole suke yi sauri don neman kariya don kar su afka cikin bala'in idan na'urar ta tashi. Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da rahoton a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a. Ya ce, rundunar ta samu nasarar tarwatsa na’urar ne ta hanyar kungiyar masu binciken fashewar abubuwa (EOD), ya kara da cewa an fara bincike don gano wadanda ke da hannu a lamarin. Ya ce wani mazaunin yankin ne ya gano na'urar a lokacin da ya je daji don sauƙaƙa kansa da misalin ƙarfe 5 na safiya...
Yanzu-Yanzu: Bom ya tashi a cocin Mahaifin gwamnan Rivers

Yanzu-Yanzu: Bom ya tashi a cocin Mahaifin gwamnan Rivers

Uncategorized
Rahotanno daga jihar Rivers na cewa Wasu bata gari sun saka Bam a cocin mahaifin gwamnan Jihar, Nyesom Wike dake babban birnin jihar, Fatakwal.   Rahoton wanda TheNation ta kawo yace wanda suka kai harin su 5 ne inda suka shiga cikin cocin me suna Christian Universal Church International da yammacin jiya, Asabar inda suka saka ababen fashewar wanda ake tsammanin nakiyoyine.   Tashin bam din ya lalata cocin sosai, a cewar Rahoton wanda hakan ya matukar saka fargaba a zukatan mutanen yankin.   Babu dai wana kungiya data dauki alhakin abin amma an kama 2 daga cikin wanda suka kai harin inda aka mikasu hannun 'yansanda.