
Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga
Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga har zuwa ranar biyu ga watan Afrilu.
A karon farko a tarihin wasannin Bundesliga na Jamus a wannan makon an gudanar da wasanni ba tare da 'yan kallo a filayen kwallo ba. A waje guda kuma mahukunta sun ce an jingine wasannin a sakamakon tsoron yaduwar cutar Coronavirus. Dakatar da wasannin ya shafi har da wasannin da aka shirya gudanarwa a karshen makon nan.
Rahoto daga DW Jamus