
Hotuna: Yanda Musulmai Dubu 10 suka taru dan addu’ar neman tsari da Coronavirus/COVID-19 a Bangladesh
Musulmai a kalla miliyan 10 ne a kasar Bangladesh suka taru a wani fili inda suka yi sallah da karatun Qur'ani dan neman kariya daga cutar nan data addabi Duniya watau Coronavirus/COVID-19.
Saidai hukumoni sun shaidawa manema labarai cewa masallatan sun yi taronne ba tare da sanin hukuma ba.
Akwai dai fargabar cewa wannan taro ka iya habbaka yaduwar cutar tsakanin 'yan kasar.
Mutum 1 ya mutu a kasar sanadiyyar cutar.