
Kwanannan Yan Najeriya Miliyan 15 zasu fada Talauci>>Bankin Duniya
Bankin Duniya da kuma shugaba kwamitin dake baiwa shugaban kasa Shawara akan tattalin arziki sun yi gargadin cewa sai gwamnati ta tashi tsaye wajan magance matsalar tattalin arzikin da kasar ta samu kanta a ciki dan kare aukuwar matsaloli nan gaba.
Bankin Duniyar da Dr. Doyin Salami sun bayyana hakane a wajan wata ganawa da aka yi kan habaka tattalin arziki ta kafar sadarwa.
Bankin Duniyar yace nan da shekarar 2022 'yan Najeriya Miliyan 15 zuwa 20 ne zasu fada kangin Talauci.
Wakiliyar bankin Duniyar, Joseph Raji ta bayyana cewa zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ya taba gwamnatin Najeriya sosai inda aka ga koma bayan tattalin arziki wanda ba'a taba ganin irinsa ba tun shekarun 1980s. Ta bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin tarayyar ta saukaka yanda h...