fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Bara

Allah Sarki: Bidiyon wulakancin da wani yawa yara mata dake bara sanye da Hijabi ya dau hankula

Allah Sarki: Bidiyon wulakancin da wani yawa yara mata dake bara sanye da Hijabi ya dau hankula

Uncategorized
Allah sarki, wasu kananan yara mata dake sanye da Hijabi sun tunkari wani mutum dake zaune a cikin mota dan yin bara.   Saidai wata irin harara da ya daka musu da tabe baki ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda wasu ke bayyana hakan da cewa ya fi yaran bukatar kudin.   Saidai wasu sun yi Allah wadai da abinda mutumin yayi inda suke cewa da basu hakuri yayi da yafi.  
Mabarata 648 ne aka kama a Kano saboda ci gaba da barar duk da hanin Gwamnati

Mabarata 648 ne aka kama a Kano saboda ci gaba da barar duk da hanin Gwamnati

Uncategorized
Daga watan Fabrairu zuwa yanzu, Hukumar Hizbah a jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mabarata 648 da shka ci gaba da barar duk da yake cewa gwamnati ta haramta hakan.   Kakakin Hukumar, Lawal Ibrahim ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace an kama mabaratan a bangarori daban-daban na jihar. Yace 416 daga ciki matane sai kuma sai kuma 232 mazane inda yace zasu ci gaba da farautar mabaratan da suke take dokar da gwamnati ta saka.   Yace suna kan tantance mabaratan da aka kama kuma wanda wannanne karin farko na Laifin nasu za'a mikasu ga danginsu wanda kuma dama sun taba taka dokar za'a gurfanar dasu a kotu.

Ku roki gwamnati ba Mutane ba, Sarki Sunusi Ya fadawa masu rokon Sadaka

Siyasa
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Musulunci bai yadda da baraba,  Sarkin kano kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne ya bayyana hakan a babban taron kasa na Alarammomi (Makarantan kur’ani) da ya gabata a ranar Asabar. Kamar yadda Sahara repoter ta rawaito  Sarkin ya kuma bayyana cewa yakamata masu rokon da su mika  rokonsu ga gwamnati ba wai mutane da ke kusa da su ba.  Ya ce, "Haramun ne kuma hanine  a cikin addinin Musulunci yin roko, a cewar sa idan dole ne a nemi sadaka to zaifi kyau a roki gwamnati, ba mutane dai dai Ku ba,  Ya kuma shawarci masu wannan hali da cewa Zai fi kyau a gare su da suna saro itacen wuta su sayar don samun abin da suke bukata fiye da yin roƙo.  Ya ja hankalin masu wannan dabi'a da cewa “Wadanda suka mai da roko Sana'a to...