
Da Dumi Duminsa: Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama ya kamu da cutar Covid-19
Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya bayyana cewa ya kamu da cutar Covid-19 ranar lahadi.
Inda ya kara da cewa yayi rigakafin cutar tare da matarsa Michelle Obama, kuma ita bata kamu da cutar ba.
A karshe Obama yace kamuwa dayayi da cutar ya kamata ta zama izna ga wa'yanda basuyi rigakafin ba da suje su duk da cewa an samj saukin cutar.