fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Tag: Baranci ga Annabi Muhammad(SAW)

Ban ce na daina Bugawa Faransa Kwallo ba>>Pogba

Ban ce na daina Bugawa Faransa Kwallo ba>>Pogba

Wasanni
Tauraton dan kwallon kungiyar Manchester United,  Paul Pogba ya bayyana cewa bai ce ya daina bugawa Kasar Faransa Kwallo ba.   A baya dai an ruwaito cewa saboda maganar da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yayi ta nuna goyon bayan batanci da akawa Annabi Muhammad(SAW) ta hanyar zanen Barkwanci, Pogba yace ya daina bugawa Faransa Kwallo.   Cikin wanda suka ruwaito wannan Labari akwai TheSun, saisai Pogba ta shafinsa na Instagram ya bayyana cewa ba gaskiya bane wannan labari.   Pogba yace labarin ba gaskiya bane kuma yana Adawa da duk wani harin ta'addanci sannan Addininsa na daga cikin mafiya son zaman lafiya kuma dolene a kareshi. Pogba ya zargi jaridar da yi masa karya sannan yace zai dauki matakin Shari'a akai saboda wannan lamarine bana wasa ba. ...