fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Barayin

Hotuna: Fusatattu sun kashe tare da kona wasu barayi da aka kama a Calabar

Hotuna: Fusatattu sun kashe tare da kona wasu barayi da aka kama a Calabar

Uncategorized
Wasu barayi da aka kama a daren jiya a birnin Calabar na jihar Cross-River sun gamu da fushin matasa inda suka kashesu tare da banka musu wuta.   Lamarin ya farune a titin Marian Road da misalin karfe 9 na yamma. Matasan da duka basu kai shekatu 20 ba sun shiga babban shagon siyayya na Sunnytex, saidai jama'ar gari sun afka musu.   Wani shaida ya bayyana cewa, sun lura matasan bindigar gargajiya ce suke rike da ita shiyasa suka afka musu, yace bayan fitowarsu daga shagon siyayyar sai suka bisu, daya daga ciki ya so sajewa da jama'ar gari inda shima ya rika ihun barawo amma aka ganoshi.   An kamashi da wani karin barawon daya inda aka kashesu da kuma kona gawarsu.