fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: Barkwanci

An kai mai barkwanci kotu kan yi wa shugaban kasa dariya

An kai mai barkwanci kotu kan yi wa shugaban kasa dariya

Siyasa
Wani mai wasan barkwanci a Tanzaniya Idris Sultan ya bayyana a gaban kotun majistare da safiyar ranar Laraba a birnin Dar es Salaam, kwana takwas bayan kama shi. Za a tuhumi Sultan da laifukan intanet, da lalata shaidu da kuma amfani da layin wayar da aka yi wa rijista da sunan wani, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda ya shaida wa BBC ranar Litinin. A ranar Talatar makon da ya gabata ne aka kama shi, bayan da wani bidiyo ya yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta, inda aka ga mai barkwancin yana yi wa wani tsohon hoton Shugaba John Magufuli dariya. 'Yan sanda sun zarge shi da keta dokar laifukan intanet da kuma tsokanar shugaban kasa, a cewar lauyansa Bennedict Ishabakaki. Mafi yawan masu amfani da shafukan...