
Gwamnati ta yi magana kan dalilin rashin fara aikin tashar ruwa ta Baro dake Naija, watanni 17 bayan da shugaba Buhari ya kaddamar da ita
Rashin kyawun titin dake kaiwa ga tashar ruwa ta kan tudu ta Baro dake jihar Naija ya hana tashar fara aiki watanni 17 bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da ita.
Hukumar kula da ruwayen Najeriya, NIWA ta bayyana cewa tana aiki tukuru wajan ganin ta tuntubi hukumomin da suka kamata dan ganin an gyara titin kuma tashar ruwan ta fara aiki.
Shugaban Hukumar, Dr. George Moghalu ne ya bayyana haka ga Dailytrust a ganawar da suka yi dashi a Lokoja.
Yace tashar na da matukar muhimmaci ga ayyukan sauran tashoshin kan Tudu na Kaduna da sauransu.
Etsu Nupe da Gwamnan jihar Naija duk sun koka akan rashin kammala wannan hanya da zata kai ga tashar ruwan.
Shugaban hukumar NIWA, Dr. George yace yana duba yiyuwar tuntubar gwamnan...