
A yau an daura aure na da Halima Nwakaego, Inshi Bashir El-Rufai: Pantami, Muhammad Sanusi II, Sule Lamido, Nuhu Ribadu da sauransu sun halarta
A yau, Asabar, 21 ga watan Nuwamba na shekarar 2020 an daura auren dan gidan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai da matarsa, Halima Ibrahim Kazaure, 'yar gidan sanata Ibrahim Kazaure a Abuja.
Bashir ya saka hotonsa tare da masoyiyarsa inda yace sun yi nasara.
Manyan baki irin su ministan Sadarwa da tattalin arzikin Zamani, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami da Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, Tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu da sauransu sun halarci wajan bikin.
Bashir ya bayyana farin cikinsa da wannan rana sosai inda kuma dan uwansa, Bello ya tayashi Murna.
https://twitter.com/BashirElRufai/status/1330173923103739907?s=19
https://twitter.com/BashirElRufai/status/133020282953394586...